Bagobiri mai kaji

Wata rana wani Bagobiri ya zuba kaji a cikin keji yana yawo da su don ya sayar, har ya gaji da daukar su. A zuciyarsa sai ya ce: “Na ga alama kajin nan nema suke su mutu saboda zafi, kamata ya yi na sake su su tafi da kafafunsu zuwa wurin da na nufa.” Daga […]

Bagobiri mai kaji
Bagobiri mai kaji

Wata rana wani Bagobiri ya zuba kaji a cikin keji yana yawo da su don ya sayar, har ya gaji da daukar su. A zuciyarsa sai ya ce: “Na ga alama kajin nan nema suke su mutu saboda zafi, kamata ya yi na sake su su tafi da kafafunsu zuwa wurin da na nufa.” Daga nan sai ya bude wa kaji kofa, keji kuwa suka fito fir-fir, kowacce ta kama gabanta sai Basakwace ya dauki sanda ya bi wani zakara a guje yana cewa: “Allah wadaranka, kai da kake iya banbancewa tsakanin lokacin asuba da tsakar dare amma yanzu ka kasa gane hanya da rana tsaka.”
Daga Anti Halima Shata Katsina, 08131014066