Bahadeje a Ingila
Wani Bahadeje ne ya je Ingila, yana yawo a gari sai kashi ya matse shi. Ga gari tsaf-tsaf, ba wurin tsuguno kuma abin ka da baƙo, bai san bayi/kewaye a yankin ba, sannan ba ya son ya tambaya don kar a ce sai ya biya. Ya sami bayan wata fulawa da aka shuka don kwalliyar […]
Wani Bahadeje ne ya je Ingila, yana yawo a gari sai kashi ya matse shi. Ga gari tsaf-tsaf, ba wurin tsuguno kuma abin ka da baƙo, bai san bayi/kewaye a yankin ba, sannan ba ya son ya tambaya don kar a ce sai ya biya. Ya sami bayan wata fulawa da aka shuka don kwalliyar gari, ya tsuguna bayanta, ya shiga tottotsa kashi abinsa.
Ashe wasu ’yan sanda da ke yin sintiri a wannan yankin sun hange shi ya daɗe a tsugune bayan fulawa shi kaɗai. Suka nufi wurin, shi kuma da ya hango su, sai ya yi wuf ya ciro hularsa (irin ta kaboyi) ya kife kashin nasa da ita, sa’annan ya yi maza ya gyara wandonsa. Da suka zo suka tambaye shi dalilin daɗewarsa a bayan fulawa a tsugune, sai ya ce tsuntsunsa ne ya gudu daga cikin kejinsa, shi ne ya zo nan wajen fulawar ya kama shi, ya kife da hula amma bai san yadda zai yi har ya je ya ɗauko kejinsa ya mayar da shi ciki ba, tun da ba wanda zai taimaka masa.
Sai Turawan ’yan sandar nan suka ce to ya yi maza ya tafi gidan nasa ya ɗauko kejin, za su taimaka masa a sanya shi ciki. Nan take Bahadeje ya yi tafiyarsa abinsa, ya bar Turawan nan da tulin kashi kife a hula.
Can da suka ga ya daɗe bai dawo ba, sai suka yanke shawarar kama tsuntsun su tafi da shi ofis, idan ya dawo ya biyo su can ya karɓi abinsa, tun da za su rubuta rahoto. Sai ɗan sanda daya ya ce wa ɗayan: “Ka ɗaga mani hular a hankali, ni kuma zan yi suka in dira in kama shi.” Haka kuwa aka yi, watau ɗan sandan na ɗaga hular nan sai ɗayan ya buga rida, ya dira a ƙarƙashin hular da hannuwansa biyu, da nufin kama ɗan tsuntsu. Sai caɓal! Duk ya bi ya damalmale a kan tulin kashin nan mai shegen doyi.