Bahadeje da matarsa
Wani Bahadeje ne yana zaune da matarsa suna hira sai ta ce: “Bari na kawo maka abinci ka ci, na ga yanzu ka dawo daga kasuwa.” Sai ya ce: To, uwargida me aka dafa ne yau?” Sai ta ce: “Shinkafa da miya.” Sai ya ce: “In ce dai ba a gidan makwabcinmu kika sayo tumatur […]
Wani Bahadeje ne yana zaune da matarsa suna hira sai ta ce: “Bari na kawo maka abinci ka ci, na ga yanzu ka dawo daga kasuwa.” Sai ya ce: To, uwargida me aka dafa ne yau?” Sai ta ce: “Shinkafa da miya.” Sai ya ce: “In ce dai ba a gidan makwabcinmu kika sayo tumatur din ba ko?” Sai ta ce: “Kamar ka sani kuwa, a can na sayo ke nan yaya zan yi?” Sai ya ce: “Ina tsoro ko ya sa guba a cikin tumatur din.” Sai ta ce: “Ai sai da na ba karen gidan nan tukuna na kawo maka maigida.” Ya ce: “To, shi ke nan.” Ya fara cin abincin ke nan sai ’yar aikin gidan ta shi go ta yi sallama, ta ce: “Alhaji! Mai gadi yace a fada maka wai karen gidan nan ya mutu.” Nan take Alhaji ya karaya, sai ya ce da matarsa: “Kafin na mutu zan roki gafararki, domin na yi miki laifi, mun haifi yara biyu da ’yar aikin gidan nan.” Sai matar ta ce: “Ni ma ka yi mini gafara, a cikin yaranka 6, guda 4 na mai gadi ne, 2 ne kawai naka.” Ana haka sai ga mai gadi ya shigo ya ce: “Alhaji, wani ne ya yi sallama a waje yanzu, koda na amsa sai yake gaya mini cewa a ba ka hakuri, shi ne ya buge karen nan da mota har ya mutu.”
Daga Mudassir Maishayi Ningi, 08169139393