Bai dace a rika maganar zaben 2019 yanzu ba – Tambuwal
Gwamnan Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a zantawarsa da manema labarai, ya yi magana a kan zaben 2019 da wasu ayyukka na gwamnatinsa da sauran bayanai masu muhimmanci. Ga yadda zantawar ta kasance: A shekara biyu da rabi na mulkin shugaba Buhari me Jihar Sakkwato ta amfan kuma ina aka kwana kan tashar wuta […]
Gwamnan Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a zantawarsa da manema labarai, ya yi magana a kan zaben 2019 da wasu ayyukka na gwamnatinsa da sauran bayanai masu muhimmanci. Ga yadda zantawar ta kasance:
A shekara biyu da rabi na mulkin shugaba Buhari me Jihar Sakkwato ta amfan kuma ina aka kwana kan tashar wuta mallakar jihar?
Shugaba Buhari alkawari uku ya yi wa mutanen Najeriya: yaki da cin hanci da rashawa da tsaro da farfado da tattalin arziki. A kan wadannan, kasar ta amfana da kokarin da shugaban kasa ke yi na ganin an samu zaman lafiya, hare-haren boko haram ya ragu sosai jefi-jefi ne kawai kake jinsu a Borno da Adamawa. Magance matsalar cin hanci ma abu ne da zai taimaka. A bangaren hanyoyin mota tun kafin ya zo Sakkwato zuwa Illela, da Jega da kuma zuwa Sabon birni duk lafiya lau suke zuwa Gusau ce ni da gwamnan Zamfara muka yi wa faci-faci. Ci gaban jama’a kuma mun amfana da mulkin shugaba Buhari domin ya ba mu kudin tallafin biyan albashi da da kudaden masu ritaya da kyautatawa ma’aikata na Paris Kulob, mun bi umarninsa mun biya ma’aikata tun daga kananan Hukumomi zuwa jiha, sauran kudin mun kammala manyan ayyuka da muka bude su a watan Mayun bara.
Maganar tashar wuta mallakar jiha muna kan kokarinmu, don kowa ya san masu zuba jari ba za su zo wurin da babu wutar lantarki ba, muna kan yin abin da zai kawo wuta a jihar. An kammala kashi 80 a yanzu na aikin.
Sakataren gwamnati ya zauna da wasu masana suke fada masa gwajin wutar kawai na bukatar a sayi man dizal na miliyan 500, don wannan ne muke shawarar canja man da za mu rika amfani da shi bayan kammala aikin don saukin tafiyar da ita, kwamitin Injiniya Bello Suleiman da muka kafa ya sanar da mu sauran aikin yana bukatar 1.7 biliyan kafin a kammala, ina sanar da jama’a da zaran mun samu kudin za a kammala aikin cikin wata takwas.
Gwamnati ta kaddamar da dokar tabaci a bangaren ilimi amma har yanzu ana fama da rashin kayan karatu a dakunan karatu da lalatattun ginoni da rashin kujerin zama wane amfani dokar ta samar?
Na yarda, amma ina son ka je kwalejin ilmi ta Shehu Shagari da ta kiwon lafiya na Gwadabawa ka ga irin sauyin da muka samar. A rahoton kwamitin da muka sanya ya sheda mana, makaranta 400 da ke bukatar gyara za su lakume kudi biliyan 40, cikin makaranta 2300 da muke da su. Maganar kudi ce da ake nema a shirin suna da yawa kan haka mun fara magana da bankin duniya da ya tallafa mana. Ba abu ba ne da za a kammala a lokaci daya. Muna kan kokarinmu muna sane da halin da suke ciki, muna bukatar kudi ne.
Ina aka kwana kan batun bashin da bankin masana’antu zai rabawa ‘yan kasuwar Sakkwato, kuma yanzu sama da shekara 7 da gadar Bafarawa ta yanke a duk damuna ruwa na raba sama da gari 27 da karamar Hukumar Isa ko akwai wani shiri da ake yi?
A batun bashin ‘yan kasuwa, mun biya kudin bangarenmu ga bankin masana’antun ya nema don fitar da kudin a baiwa ‘yan kasuwarmu, kusan shekara daya yanzu sai dai mun hakikance dole ‘yan kasuwa na gaskiya ne za a baiwa bashin ba wani dan siyasa da zai amfana da shi, don bunkasa kasuwanci a Sakkwato ne, muna kan wannan.
Hanyar Isa Bafarawa tana cikin kasafin kudi na badi. Jami’an gwamnati da na tsaro suna aiki sosai a wurin don kawar da batagarin da suke addabar yankin.
Ko zaka sake tsayawa takarar gwamnan Sakkwato a zaben 2019. Sanna kuma gidajen gwamnati da za a sayarwa ma’aikata suna korafin kudin da lokaci?
Maganar zaben 2019 a yanzu kawar da hankali ne da rashin kyautatawa wadanda ke rike da mukaman gwamnati. Yanzu lokacin da ya kamata a tattauna yadda jagoranci ke tafiya a ragamar da aka damka musu a 2015.
zaben 2019 akwai fiye da shekara kafin zaben, a 2017 muke a yanzu. Za mu yi maganar zaben idan lokacinsa ya zo, amma yanzu ana jagoranci ne, don haka ayi maganar shugabanci ba zabe ba. Bai dace a rika kawar da hankalin shugabanni ba. Maganar gidaje kuma mun bada farashi sakui, lokaci kuma idan ka kwatantashi da sauran jihohi shi ne mafi nisa da aka ba ma’aikaci ya biya kudinsa. Mun yi iyakar kokarinmu kan wannan.