Bai dace Buhari ya ziyarci Birtaniya a halin rashin tsaron Najeriya- PDP
Babbar jam’iyar hamayya a Najeriya, PDP, ta soki ziyarar kashin-kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi yanzu a kasar Birtaniya, ta na mai cewa, hakan ba daidai ba ne, duba da yadda matsalar rashin tsaro ke kara ta’azzara a kasar. Jam’iyyar PDP ta ce, a matsayinsa na shugaban kasa, dole ne ya tsaya tsayin […]
Babbar jam’iyar hamayya a Najeriya, PDP, ta soki ziyarar kashin-kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi yanzu a kasar Birtaniya, ta na mai cewa, hakan ba daidai ba ne, duba da yadda matsalar rashin tsaro ke kara ta’azzara a kasar.
Jam’iyyar PDP ta ce, a matsayinsa na shugaban kasa, dole ne ya tsaya tsayin daka, dan tabbatar da an dakile matsalolin tsaron da ke addabar wasu jihohin kasar nan.
A wani taron manema labarai da PDP ta kira, a yau Juma’a, shugaban jam’iyar PDP Uche Secondus, ya ce ziyarar da Buharin ke yi a Landan din, ba dan muradin kasa yake yin ta ba, a kashin kansa ne kawai.
Uche Secondus, ya koka kan yadda kashe-kashen gilla da ke faruwa a jihohin Zamfara da Benuwe da Taraba da ma wasu jihohin da dama, lallai ne gwamnati ta takawa abin birki. In ji shi.