Bai kamata a bar harshen Hausa ya durkushe ba – Farfesa Mustapha
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Abdullahi Mustapha ya bukaci masu ruwa da tsaki ga ci gaban harshen Hausa su tabbatar harshen bai samu wata nakasa ba. Farfesa Abdullahi Mustapha ya yi wannan kira ne a lokaci bikin makon Hausa da Tsangayar Harsunan Afirka da Sashin Harshen Hausa na jami’ar suka gudanar a […]
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Abdullahi Mustapha ya bukaci masu ruwa da tsaki ga ci gaban harshen Hausa su tabbatar harshen bai samu wata nakasa ba.
Farfesa Abdullahi Mustapha ya yi wannan kira ne a lokaci bikin makon Hausa da Tsangayar Harsunan Afirka da Sashin Harshen Hausa na jami’ar suka gudanar a makon jiya.
Farfasa Mustapha wanda ya samu wakilcin shugaban sashin kula da al’amuran dalibai na jami’ar Farfesa Mohammed Shehu, ya ce yin kiran ya zama wajibi saboda yadda harshen Hausa ke da muhinmanci a duniya.
Ya nuna gamsuwa bisa yadda ’ya’yan kungiyar habaka harshen Hausa na jami’ar suke shirya taron wanda ya ce wata hanya ce da za ta bunkasa harshen tare da kare al’adun Hausawa.
A sakon Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina Hajiya Fatima Shema da Kwamishinar Harkokin Mata, Hajiya Amina ta wakilta ta bayyana harshen Hausa a matsayin harshen da duniya ke alfahari da shi.
Shi ma a sakonsa Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar wanda Tambarin Daura Alhaji Yakubu Mohammed ya wakilta ya ce, jami’ar Ahmadu Bello abar alfahari ce gare su kuma za su yi duk mai yiwuwa don taimaka wa jami’ar.
A jawabin Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris kira ya yi ga iyaye su karfafa wa ’ya’yansu gwiwa wajen neman ilimin addini da na zamani domin ci gaban kasa.
A kasidarsa mai taken Habaka Hausa da Yayatata Hausa a Duniyar Yau, Farfesa Halliru Ahmed Amfani na Tsangayar Harsuna na Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato, ya jawo hankalin masu nazarin Hausa ne kan bambancin da ke tsakanin habaka Hausa da yayata Hausa.
Ya ce masana ilimin harshe sun nuna cewa nan gaba wasu harsuna da yawa za su mutu, kuma kililan din da za su kai labari, tilas ne a samu gwarzon harshe a cikinsu.
Farfesa Amfani ya ce “Alkaluma sun nuna cewa harshen Ingilishi ne wannan gwarzon harshe, dalili shi ne sabon tsarin nan na cure duniya waje guda (globalization) yana da abin da ke dauke da shi. Wannan abu shi ne intanet, ta hanyar intanet ne ake tsukantar da duniya. Intanet din nan yana da harshen da ke gudunar da shi. Harshen shi ne Ingilishi. Haka kuma duk mai son ya yayata hajarsa a duniyar yau, musamman ma ta hanyar intanet don sakon ya kai ga kowa, to, lallai sai ya yi amfani da Ingilishi.”
kasida ta biyu kan Adabin Hausa, mai taken: Jiya da Yau: Me ke Faruwa? Dokta Adamu Ibrahim Malumfashi na Sashin Nazarin Harshen Hausa na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ne ya gabatar da ita.