Bai kamata a sake zaben Buhari ba- PDP
Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC sun gaza matuka, da bai ka a sake zabensa ba. Secondus ya yi wannan jawabin ne ta hannun wani mataimakinsa Shehu Yusuf Kura, inda ya ce jawaban Shugaba Buhari a Landan masu karo da juna sun nuna cewa Buhari bai […]

Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC sun gaza matuka, da bai ka a sake zabensa ba.
Secondus ya yi wannan jawabin ne ta hannun wani mataimakinsa Shehu Yusuf Kura, inda ya ce jawaban Shugaba Buhari a Landan masu karo da juna sun nuna cewa Buhari bai da tabbaci idan zaben 2019 ya zo kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
“Ina tabbatar muku da cewa da ace Buhari ya yi kokari sosai, da ace gwamnatinsa ba ta karya mana tattalin arziki ba, da gwamnatinsa raba mana kai ba wanda ya yi sanadiyar yawan rikice-rikice da gwamnatinsa ba ta ci amanar mutane ba. Da Buhari ba zai ji tsoron kowane dan takara ba.”