Bai kamata Bamanga Tukur ya kira kansa Messi ba – Jimeta
Alhaji Sale Suleman Jimeta wani dan kasuwa ne mazaunin Kalaba da ya nuna damuwarsa game da furucin da ’yan siyasa suka rika yi, wa lau suna kan mulki ko kuma ba a damawa da su. a hirarsa da Aminiya . Ga dai yadda hirar ta kasance:Aminiya: An kada gangar siyasa jam’iyyu har sun yi zaben […]
Alhaji Sale Suleman Jimeta wani dan kasuwa ne mazaunin Kalaba da ya nuna damuwarsa game da furucin da ’yan siyasa suka rika yi, wa lau suna kan mulki ko kuma ba a damawa da su. a hirarsa da Aminiya . Ga dai yadda hirar ta kasance:
Aminiya: An kada gangar siyasa jam’iyyu har sun yi zaben fitar da gwani a takarar mukamai daban-daban, ya kake kallon salon siyas a da zaben 2015?
Alhaji Sale: A nan ina son jawo hankalin duk wani dan siyasa, musamman ’yan siyasar mu na Arewa wajen tafka kura-kurai da suke yi na furta irin kalamai, da suke yi, ba mu sani ba wani lokaci ko dadin mulki ne yake rudin su ko kuwa oho dai ba mu sani ba.
Aminiya:Ka na nufin wasu ’yan siyasar sun rika furta kalaman batanci ko tunzura jama’a?.
Alhaji Sale: Matsalar ita ce ka ga wasu ’yan siyasa manya a kasar nan, musamman a jam’iyya mai mulki, wato PDP, lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Hamman Yero Nyako ya samu matsala a tsakanin PDP da Jam’iyyarsa ta APC, wadda takai ma karshe aka tsige shi, aka yi wani jigo, kuma shugaban jam’iyyar PDP na kasa na wancan lokaci, wato Alhaji Bamanga Tukur, wanda shi ma dan asalin jihar ne, ya fito fili a kafafen yada labarai na kasashen ketare, yana bugun kirji yana cewa “shi Messi ne” a matsayinsa na dattijo, kuma ana ganinsa matsayinsa na shugaba ne, musamman ma a jam’iyya mai girma kamar PDP, wadda ita ce ke mulkin kasar nan bai dace ba, da abin da ya fadi su rika yin kalamai masu kyau; masu ma’ana da suka dace, ba don komai ba, sai don zaman lafiya da ci gaban kasar nan, ba wai don burinka an kori wani dan uwanka a mulki ba; ko anci masa zarafi ba. Zaman lafiyar mu shi ne ci gaban mu a kasar nan .
Aminiya: Zargin da kake yi kana jin ko akwai wasu kalamai ne da shi tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Bamanga Tukur ya furta wanda a matsayinsa na babba, jagora bai kamata ba ace ya yi su?
Alhaji Sale: kwarai kuwa.
Aminiya: Kamar me ya ce ?
Alhaji Sale: Lokacin da suka tsige Baba Mai mangoro, duk da ba a son ranmu ba ne aka tsige shi ba, kuma an yin haka ne, don son ran su ba rashin aiki ko ci gaba ba ne. Gwamnan ba ya yi ba a jihar ya fito fili, yake cewa shi Messi ne, yadda yaso haka zai juya akalar PDP da ’yan jam’iyya .
Aminiya:Kana nufin ’yan siyasa dai su rika taunawa kafin su furzar da abin da suka kunsa a baki a kalaman su?
Alhaji Sale: Eh! Yauwa abin da nake nufi ke nan manufar ke nan. Kowa ya rika sanin irin maganganun da zai fada wa jama’a, don dan Adam abin da ka fada masa zai rike shi a zuciyarsa, wata rana ba ka san abin da zai kasance da kai ba, kamar yadda yanzu ya faru da Messin PDP. Ba ya mulkin a PDP, yanzu a ina ne zai je ya zama Messi kuma? Matsayinsa na dattijo idan ma zai yi kwatance, ya siffanta kansa da wani mutumin kirki ,sai ya siffanta kansa da dan kwallo kafa wannan kuskure ne ni a nawa tunanin .
Aminiya: Kai dan asalin Jihar Adamawa ne, mazaunin Kurmi an samu sauyin takun siyasa tsakanin APC da PDP, ga alama iskar siyasar da ke kadawa na neman sauyawa, wane tsokaci zaka yi?
Alhaji sale: Mu dai gaba daya muna fatan alheri garemu. Mu dauki duk wanda ya ci namu ne, ba wai fatan mu duk wanda ya ci a zo, a yi ta fada a jihar. Duk wanda Allah ya bai wa mulki a APC ne ko PDP ne, fatan mu wanda zai kawo mana ci gaban jihar da zaman lafiyarta muke nema . Allah kum ya kawo mana shi.
Aminiya: Ana zargin ku ’yan Adamawa kamar kanku a siyasance ba a hade yake ba shi yasa ake ta takamma, ko me zaka ce ?
Alhaji Sale: Abin da zan ce akan wannan a wajen manyan mu, manyan ’yan siyasa ke nan ba mutanen jaihar ba.
Aminiya: Wato ku mabiyan ba haka ba ne ?
Alhaji Sale: A’a, ba haka ba ne a wurin mu, mu mabiyan kan mu a hade yake,manyan mu ne suke ta wannan. Duka muna fata Allah ya ba su hadin kai, ya hada kawunan su
Aminiya: Wata biyu masu zuwa idan Allah ya yi nufin mu da gani za a yi zabe, wane sako kake da shi ga ’yan Najeriya, musamman ’yan’yan jiharka ta Adamawa?
Alhaji Sale: Kowa ya kwantar da hankalinsa, a yi zabe lafiya, kar a kashe kowa, kar a kona dukiyar kowa. Don Allah a kwantar da hankali ka da a yi kashe-kashe, idan an kashe wani a Adamawa, mu ne fa muka ragu. Allah ya sanya a yi zabe lafiya; Ya kwantar mana da tashin hankali da rikici a daukacin dajeriya da Jihar Adamawa.