Bai kamata batun jagoran APC ya jawo mata rikici ba – Damboa
Wani dan siyasa kuma dan kasuwa da ke Abuja Alhaji Adamu Damboa ya shawarci magoya bayan Jam’iyyar APC musamman a yankin Arewa maso Yamma su ajiye batun neman mukami, su yi aikin da jam’iyyar za ta tsaya da kafafunta ta samu nasarar ceto kasar nan a shekarar 2015.Alhaji Adamu Damboa wanda aka fi sani da […]

Wani dan siyasa kuma dan kasuwa da ke Abuja Alhaji Adamu Damboa ya shawarci magoya bayan Jam’iyyar APC musamman a yankin Arewa maso Yamma su ajiye batun neman mukami, su yi aikin da jam’iyyar za ta tsaya da kafafunta ta samu nasarar ceto kasar nan a shekarar 2015.
Alhaji Adamu Damboa wanda aka fi sani da Damboa One ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da wakilinmu a Abuja, inda ya ce yadda ’yan siyasa a jihohin Kano da Sakkwato suke kokarin farraka jam’iyyar tun ba ta kafu ba, abin takaici ne.
Ya ce, an kafa Jam’iyyar APC ne da niyyar ceto Najeriya daga halin kunci da rashin alkiblar da take ciki, don haka bai kamata magoya bayan jam’iyyar su fara saka da mugun tsare ba. “Mu ne muka kafa Jam’iyyar PDP, an ba ni shugabancin PDP na yankin Bwarina ki na ce ban kai ba, na ba Malam Buhari. Kuma da muka hango ba za ta iya kai kasar nan tudun mun tsira ba, muka fice muka mara wa Janar Buhari baya a zaben 2003, kuma har zuwa yanzu muna tare da shi,” inji shi.
Ya ce tunda al’adar siyasar kasar nan ta ajiye gwamnan kowace jiha ya zama jagoran jam’iyya a jiharsa, ya kamata duk wani dan jam’iyya komai girmansa ya karbi hakan don a karfafa jam’iyyar. “A bar gwamnoni, su Nyako su Kwankwaso su Amaechi su Abdulfatah na Kwara su zamo jagororin APC a jihohinsu tunda su suke mulki a jihohinsu, in lokacin zaben shugabanni ya zo, kowa ya fitar da gwaninsa wanda Allah Ya ba shi a bi shi. Amma ba kawai a ce dole mu ne ’ya’yan halas don haka mu za mu zamo jagorori ba,” inji shi. Alhaji Damboa ya ce canjin nan Allah Ya kawo shi ba dabara ko karfin wani ba, “Wannan kamar gobara ce ta tashi a gidan giya za a kashe ta da giyar ce, in babu kuma kowa ya kama gudu ya tsira da ransa,” inji shi.