Bai kamata mace Musulma ta rika yawo da riga da wando ba – Amirar FOMWAN
Shugabar kungiyar Mata Musulmi ta kasa (FOMWAN) reshen Jihar Nasarawa Barista Hannatu Ahmed Muhammed ta ce bai kamata mace Musulma ta rika yawo da riga da wando ba, maimakon hijabi. Barista Hannatu Muhammed ta yi wannan gargadi ne a wurin wani taro da kungiyar dalibai Musulmi (MSS) ta kasa reshen jihar ta shirya kan muhimmancin […]
Shugabar kungiyar Mata Musulmi ta kasa (FOMWAN) reshen Jihar Nasarawa Barista Hannatu Ahmed Muhammed ta ce bai kamata mace Musulma ta rika yawo da riga da wando ba, maimakon hijabi. Barista Hannatu Muhammed ta yi wannan gargadi ne a wurin wani taro da kungiyar dalibai Musulmi (MSS) ta kasa reshen jihar ta shirya kan muhimmancin sanya hijabi da aka gudanar a makarantar Al’imam da ke Lafiya a karshen mako jiya.
Amira Hannatu wacce ta samu wakilcin shugabar sashin da’awa na kungiyar Malama Safiya Musa ta koka game da yadda wasu mata a jihar ba su son sanya hijabi maimakon haka sai su rika sanya wanduna. Ta ce Musulunci ya haramta wa mace ta sanya tufa irin na maza, sannan hijabi yana kare mutuncin mata, “don haka ina kira ga masu sanya riga da wando suna yawo su sauya dabi’unsu, idan mata za su sanya tufafi daidai koyarwar addini, to, babu shakka jama’a za su rika mutunta su a duk inda suka samu kansu,” inji ta.