Bai kamata mu siyasantar da kashe-kashen rayuka ba-Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce bai kamata jama’a su siyasantar da kashe-kashen da suka auku kwanannan a sassan kasar nan ba. Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya yi furucin a Abuja, jiya, a taron addu’ar hadin gwiwa na darikokin coci-coci don bikin tunawa da mazan jiya na shekarar 2018. Osinbajo ya ce […]
Gwamnatin Tarayya ta ce bai kamata jama’a su siyasantar da kashe-kashen da suka auku kwanannan a sassan kasar nan ba.
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya yi furucin a Abuja, jiya, a taron addu’ar hadin gwiwa na darikokin coci-coci don bikin tunawa da mazan jiya na shekarar 2018.
Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta gano cewa wasu mutane suna son yin amfani da siyasa kan kashe-kashen da suka auku a jihar Benuwe da Ribas da Adamawa da Filato da sauransu.