Bai kamata mutane su tafi babu jagoranci ba – Sabon Halifan Gabari

Bayan rasuwar Halifan Makarantar Zauren Sheikh Ali Musa Gabari, wato Malam Sanusi Musa Gabari, an nada Malam Usman Musa Gabari, a matsayin wanda zai ja ragamar wannan makaranta da ta yaye dalibai da malaman da suka kware a ilimin kur’ani da Fikihu da Hadisi a birnin Kano. A ranar Juma’ar da ta gabata ne, wato […]

Bai kamata mutane su tafi babu jagoranci ba – Sabon Halifan Gabari
Bai kamata mutane su tafi babu jagoranci ba – Sabon Halifan Gabari

Bayan rasuwar Halifan Makarantar Zauren Sheikh Ali Musa Gabari, wato Malam Sanusi Musa Gabari, an nada Malam Usman Musa Gabari, a matsayin wanda zai ja ragamar wannan makaranta da ta yaye dalibai da malaman da suka kware a ilimin kur’ani da Fikihu da Hadisi a birnin Kano.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, wato 3 ga Muharram, 1437 (16-10-2015), bayan Sallar Magariba, Malam Isa Musa Gabari a madadin iyalai da almajiran Sheikh Musa Ali Gabari, ya bayyana amincewarsu da nadin Malam Usman Musa Gabari, a matsayin sabon Halifan mahaifinsu, inda dukkan ’ya’ya da almajiran marigayin suka yi mubaya’a ga sabon Halifan.
Sabon halifan ya bayyana wa Aminiya muhimmancin wannan jagoranci, musamman abin da ya shafi karatun addini da mu’amala a cikin al’umma.
“Ana tabbatar da irin wannan jagoranci ne a cikin al’ummar Musulmi, don kada a bar mutane su tafi kara zube. Kada mu da Allah Ya dora wa nauyin koyon ilimi da yada shi ya zama dole mu tabbatar da shugabanci ko jagoranci bisa turbar da shari’ar addinin Musulunci ta yarda a yi,” inji shi.
Malam Usman, ya yi godiya da fatan alheri ga dimbin jama’ar da suka taya su alhinin rashin marigayi Malam Sanusi Musa Ali Gabari.
Shi ma Sarkin Gida, Malam Sham’unu Musa Gabari, ya bayyana cewa, daukacin iyalai da almajiran gidansu, tun daga Babbansu Malam Mansur Musa Gabari, sun amince da jagorancin dukkan karatuttuka da makarantu da ke karkashin halifancin gidan Malam Musa Ali Gabari.
dimbin mutane a birnin Kano da wasu sassan Afirika suka taru a gidan Gabari, don nuna alhininsu ga iyalan Sheikh Musa ali Gabari, game da rasuwar halifansa, sannan suka yi fatan alheri ga sabon halifa.
Dokta Yusuf Ali, da ya ziyarci wannan gidan makaranta, ya yi musu ta’aziyya, sannan ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da kulawa da gidan Malam Musa Ali Gabari.
Mutane da yawa sun mika sakon fatan Allah Ya rika ga sabon Halifan, inda mafi yawa suka bayyana shi da saukin hali da kamewa, inda kuma aka yi hasashen samun ci gaba a lokacin halifancinsa, musamman kan al’amuran ci gaban zamani.
Malam Abba, wanda shi ne babban hadimin marigayin, ya yi addu’a tare da nuna kyawawan ta’adun marigayin.
dayyabu Muhammad (Malam Abba), wanda babban hadimi ne ga Marigayi Halifa Muhammadu Sanusi Musa Gabari, ya bayyana irin kyawawan ta’adunsa, wajen yada ilimi da kuma hulda da jama’a.
“Muna rokon Allah Ya yi jinkai ga Halifa Muhammadu Sunusi Musa Gabari da mahaifinsu Sheikh Malam Musa da sauran magabata. Allah Ya rika wa sabon Halifa Malam Usman Musa Gabari. Allah Ya ba mu kyakkyawan karshe.
Mahaifinsa Malam Musa Gabari da kakansa Malam Ali Gabari dukkansu manyan malamai ne da suka gudanar da rayuwarsu wajen nema da ba da ilmi ga al’umma. Wannan ta sanya gidansu yake da matukar kima ba ga al’ummar Jihar Kano kadai ba har ga sauran jihohi da ma wajen kasar nan.
Khalifa Malam Sunusi, ya fara karatun allo a wajen Marigayi Malam Salisu Darma (Maja Baki), daga baya ya halarci Makarantar Malam Ahmadu Bakidire, inda ya sauke Al-kur’ani mai girma. Kasancewar mahaifinsa Malam Musa a matsayin babban malami, al’umma ke kwararowa don yin karatu ilmin addinin Musulunci a wajensa. Shi ma Halifa ya yi karatu a wajen mahaifinsa a fannonin da suka hada da ilmin Fikhu da Hadisi da Tauhidi da Sira da Balaga da Nahawu da Tafsiri.