Bai kamata Shugaban kasa da gwamnoni su rufe kofofinsu ga talakawa ba – Sheikh Dikko

Dokta Hassan Abubakar Dikko, shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Filato, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce ba daidai ba ne Shugaban kasa da gwamnoni su rufe kofofinsu ga talakawan kasar nan kan mawuyacin halin da suke ciki. Ya yi gargadin cewa matukar ba […]

Bai kamata Shugaban kasa da gwamnoni su rufe kofofinsu ga talakawa ba – Sheikh Dikko
Bai kamata Shugaban kasa da gwamnoni su rufe kofofinsu ga talakawa ba – Sheikh Dikko

Dokta Hassan Abubakar Dikko, shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Filato, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce ba daidai ba ne Shugaban kasa da gwamnoni su rufe kofofinsu ga talakawan kasar nan kan mawuyacin halin da suke ciki. Ya yi gargadin cewa matukar ba su canja halayensu ba, abin da ya samu gwamnatin da ta gabata zai iya samunsu:

Aminiya: Me Malam zai ce game da yadda harkokin mulkin kasar nan suke tafiya a yanzu?
Sheikh Dikko: Babu shakka mun zabi wannan gwamnati da manufar Allah Ya rushe mana gwamnatin baya wace take azaluma ce. Wannan aiki da taimakon Allah mun yi nasara, domin Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hannun wannan gwamnati. To, amma kiran da nake yi ga gwamnatin shi ne ta san cewa rayuwa ba  gefe daya take ba. Duk da yadda muka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta sani akwai dukiyarmu a wajenta. Yau mu ji cewa an karbo kudi a hanun shugaba wane ko minista wane ko dan kwangila wane. Wannan dukiya ce ta kasa ta kuma al’umma ce. Yana da kyau kuma lokaci ya yi da gwamnatin za ta juyo ta kalli talakawan kasar nan da suka zabe ta. Ba adalci ba ne a rayuwa shugaba, ya rufe kofarsa ga talakansa. Wannan dabi’a ce mara kyau, talaka ya nemi ganin shugabansa amma abin ya gagara, saboda shugaba ya kewaye kansa da wadansu mutane wadanda aka nada ministoci ko masu ba da shawara da suke ba shi muguwar shawara. Shugaban kasa ko Gwamnan Jiha ko Shugaban karamar Hukuma duk wanda ya yi haka, bai yi daidai ba.
Shugaba ya bude kofarsa ga talaka ya zo ya ba shi shawara ya dauki na dauka ya zubar da na zubarwa shi ne ya kamata. Muddin shugabannin gwamnatin nan ba haka suka yi ba, to abin da ya kayar da gwamnatin da ta gabata, shi zai kayar da su. Don haka muke bai wa Shugaban kasa da gwamnoni da sauran masu rike da madafun iko a kasar nan, shawarar su rika sauraren koke-koken talakawan da suka zabe su. Ba a adalci ba ne talaka a shekarun baya bai sayi ruwa don ya sha ba, amma yanzu ko a karkara ne idan kana son ruwa mai kyau don ka sha, sai dai ka sayi fiya-wata. Ba daidai ba ne a ce idan rashin lafiya ya kama talaka ya je asibitin gwamnati, sai ya biya dubban Naira kafin a duba lafiyarsa, alhalin gwamnati tana kallo. Don haka yana da muhimmanci kwarai da gaske gwamnatin nan ta fahimci cewa idan ba ta magance wa talaka matsalolinsa ba, ba ta tsare masa tattalin arzikinsa ba, babu mai iya tsare masa. A yau kananan ’yan kasuwa inda za su zauna su yi kasuwanci ya gagara, domin gwamnati ta yi biris da harkokin kasuwanci, gwamnati ta yi biris da harkokin da za su taimaki talakawan kasar nan. A yanzu akwai gwamnatocin da suka ce babu ruwansu da harkokin addini, sun cire duk abin da ya shafi addini babu ruwansu. Alhali a lokacin da suke neman kuri’a malaman addini ne suka bi, don su taimaka musu a zabe su. Idan ka yi magana sai a ce maka babu kudi, alhali muna ganin irin abin kunyar da wadansu gwamnonin kasar nan suke tafkawa. A kullum ’yan jarida suna bayyana mana cewa ga wani Gwamna ya mallaki gidaje  a kasashen waje, ga wani Gwamna ya sayi motoci na fariya da sauransu, amma idan ka yi magana sai su ce maka babu kudi a kasa. Malaman addinin Musulunci da na Kirista da shugabannin jama’a da sarakuna an ce kada su yi magana. Kai ba ma wannan ba, hatta abokansu na siyasa da suka yi gwagwarmayar yakin neman zabe an jingine su a gefe.

Aminiya: Wato wannan ya nuna cewa akwai matsala ke nan a tafiyar wannan gwamnati?
Sheikh Dikko: Ni a fahimtata akwai matsala a tafiyar wannan gwamnati, don haka ya kamata su gyara. Duk wata hanya da za ta kawo walwala a kasar nan gwamnati ta san ta. Don haka gwamnati ta fito da wannan hanya mutane su bi domin su samu walwala. Idan ya zamana gwamnati ba ta damu  ba, kuma idan ka yi magana a ce maka  babu kudi a kasa, alhali mu din nan ’yan Najeriya ne. Duk irin kason kudin da aka bai wa kowace jiha a kowane wata yana fitowa a jaridu kuma muna karantawa. Idan wani Gwamna ya fito ya ce babu kudi an yi abin da ba daidai ba. Domin amanar al’ummar da suke yi wa jagoranci aka ba su. Kanawa amana ce a wajen Gwamnan Kano, mutanen Adamawa amana ne a hannun Gwamnan Adamawa, haka Gwamnan Taraba ko Gombe da sauran gwamnonin jihohin kasar nan.
Idan gwamnonin jihohin nan suka mance cewa al’ummomin jihohinsu amana ne a hanunsu, to su sani cewa za a tambaye su wannan amana da aka damka musu a gobe kiyama. Idan ka zalunci talakawan jiharka me za ka ce wa Ubangiji a gobe kiyama? Idan ka ce ba za ka saurari malaman addininka ba, yaya za ka zama mutumin kirki? Dokokin kasar nan ba bin su ake yi ba, kamar yadda ya kamata. To,  ashe ka kusanci malaman addini su fada maka gaskiya, shi ne mafi alheri. Don haka ina kira ga jagororin gwamnati a duk matakai, su ji tsoron Allah su yi adalci ga talakawan kasar nan. Wannan ne zai sa gwamnatinsu ta tabbata, amma idan suka ki yin adalci babu shakka za su riski abin babu auki. Abin da muke gaya wa gwamnati ke nan, ko ta ji ta dauka ko kada ta dauka mu dai mun fada, wannan ita ce nasihata ga gwamnati a kowane mataki, Allah Ya sa su gyara.

Aminiya: To, a karshe wannan kira kake da shi zuwa ga al’ummar kasar nan?
Sheikh Dikko: Ina kira ga al’ummar Najeriya su yi hakuri domin hakuri ba ya baci. La’anta da tsinuwa ba nasu ba ne. Allah zai bi musu kadi inda suke ganin ba a yi musu daidai ba, inda aka yi musu daidai su lura su iya ganin an yi musu daidai. Domin a kullum abin da mutane suke cewa gwamnatin nan ta yi musu.
Wannan gaskiya ne gwamnatin nan ta yi mana, amma duk yadda muke ganin gwamnatin nan ta yi mana, idan muka ga ta yi wani abu wanda ba daidai ba, dole ne mu fada. Yanzu fa wannan gwamnati ta doshi shekara biyu saura shekara biyu ta gama wa’adinta, yaushe ne aka tsaya aka yi aiki? Yaushe aka tsaya aka yi abin da ya kamata? Wannan ba daidai ba ne.

Gwamna ya sayi motoci na fariya da sauransu, amma idan ka yi magana sai su ce maka babu kuxi a qasa. Malaman addinin Musulunci da na Kirista da shugabannin jama’a da sarakuna an ce kada su yi magana. Kai ba ma wannan ba, hatta abokansu na siyasa da suka yi gwagwarmayar yaqin neman zave an jingine su a gefe.
Aminiya: Wato wannan ya nuna cewa akwai matsala ke nan a tafiyar wannan gwamnati?
Sheikh Dikko: Ni a fahimtata akwai matsala a tafiyar wannan gwamnati, don haka ya kamata su gyara. Duk wata hanya da za ta kawo walwala a qasar nan gwamnati ta san ta. Don haka gwamnati ta fito da wannan hanya mutane su bi domin su samu walwala. Idan ya zamana gwamnati ba ta damu  ba, kuma idan ka yi magana a ce maka  babu kuxi a qasa, alhali mu xin nan ’yan Najeriya ne. Duk irin kason kuxin da aka bai wa kowace jiha a kowane wata yana fitowa a jaridu kuma muna karantawa. Idan wani Gwamna ya fito ya ce babu kuxi an yi abin da ba daidai ba. Domin amanar al’ummar da suke yi wa jagoranci aka ba su. Kanawa amana ce a wajen Gwamnan Kano, mutanen Adamawa amana ne a hannun Gwamnan Adamawa, haka Gwamnan Taraba ko Gombe da sauran gwamnonin jihohin qasar nan.
Idan gwamnonin jihohin nan suka mance cewa al’ummomin jihohinsu amana ne a hanunsu, to su sani cewa za a tambaye su wannan amana da aka damqa musu a gobe Qiyama. Idan ka zalunci talakawan jiharka me za ka ce wa Ubangiji a gobe Qiyama? Idan ka ce ba za ka saurari malaman addininka ba, yaya za ka zama mutumin kirki? Dokokin qasar nan ba bin su ake yi ba, kamar yadda ya kamata. To,  ashe ka kusanci malaman addini su faxa maka gaskiya, shi ne mafi alheri. Don haka ina kira ga jagororin gwamnati a duk matakai, su ji tsoron Allah su yi adalci ga talakawan qasar nan. Wannan ne zai sa gwamnatinsu ta tabbata, amma idan suka qi yin adalci babu shakka za su riski abin babu auki. Abin da muke gaya wa gwamnati ke nan, ko ta ji ta xauka ko kada ta xauka mu dai mun faxa, wannan ita ce nasihata ga gwamnati a kowane mataki, Allah Ya sa su gyara.
Aminiya: To, a qarshe wannan kira kake da shi zuwa ga al’ummar qasar nan?
Sheikh Dikko: Ina kira ga al’ummar Najeriya su yi haquri domin haquri ba ya vaci. La’anta da tsinuwa ba nasu ba ne. Allah zai bi musu kadi inda suke ganin ba a yi musu daidai ba, inda aka yi musu daidai su lura su iya ganin an yi musu daidai. Domin a kullum abin da mutane suke cewa gwamnatin nan ta yi musu.
Wannan gaskiya ne gwamnatin nan ta yi mana, amma duk yadda muke ganin gwamnatin nan ta yi mana, idan muka ga ta yi wani abu wanda ba daidai ba, dole ne mu faxa. Yanzu fa wannan gwamnati ta doshi shekara biyu saura shekara biyu ta gama wa’adinta, yaushe ne aka tsaya aka yi aiki? Yaushe aka tsaya aka yi abin da ya kamata? Wannan ba daidai ba ne.