Bai kamata Shugaban Kasa ya rika nada shugaban INEC ba – Jega

Ya kuma bukaci a mayar da tura sakamakon zabe ta intanet ya zama wajibi

Bai kamata Shugaban Kasa ya rika nada shugaban INEC ba – Jega

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira da a yi wa dokar zabe ta shekara ta 2022 kwaskwarima.

Ya ce kodayake dokar zaben ba a taba yin irinta ba a tarihin Najeriya, akwai bukatar a yi mata gyare-gyare domin cire saɗarori masu harshen damo a cikinta.

Farfesa Jega ya bayyana hakan ne yayin wani taron kara wa juna sani da Cibiyar Bayar da Horo kan Harkokin Majalisa da Dimokuradiyya ta Najeriya (NILDS) ta shirya wa Sanatoci a Ikot Ekpene da ke Jihar Akwa Ibom ranar Asabar.

Ya ce idan aka yi kwaskwarimar, za ta tabbatar an tilasta yin amfani da na’ura wajen tura sakamakon zabe a yayin zabe na shekara ta 2027 mai zuwa.

Tsohon Shugaban na INEC ya kuma ce ya kamata a kwace damar nada shugaban hukumar daga hannun Shugaban Kasa domin tabbatar da raba hukumar da siyasa.

Ya kuma ce ya kamata a sake duba dokar ta yadda za a kammala dukkan shari’o’in zabe kafin lokacin rantsuwa.

Masu ruwa da tsaki da dama dai sun nuna damuwarsu kan yadda suka ce sashe na 64 na dokar zaben wanda ya yi bayani a kan yadda za a tura sakamakon zaben na da sarkakiyar da ya kamata a sake duba shi.

To amma Farfesa Jega ya ce ya kamata a yi wa sashen kwaskwarima domin a sanya aika sakamakon zaben ta intanet ya zama wajibi, ciki har da sakamakon rumfunan zabe da kuma takardun tattara zaben da aka yi amfani da su a matakai daban-daban.

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Lamari Game Da Harin Sojoji Kan Al’umma A Sakkwato