Bai kamata taron kasa ya kau da kai daga batun ballewa ba – Tofa
Alhaji Bashir Othman Tofa shi ne dan takarar Shugaban kasa a karkashin rusasshiyar Jam’iyyar NRC za ben 1993 da ake ganin dan kasuwar nan marigayi Moshood Kashimawo Olawale Abiola na Jam’iyyar SDP ne ya lashe shi. A wannan tattaunawa Tofa wanda jigo ne Jam’iyyar APC ya ce bai kamata a ji tsoron tattauna batun ballewa […]
Alhaji Bashir Othman Tofa shi ne dan takarar Shugaban kasa a karkashin rusasshiyar Jam’iyyar NRC za ben 1993 da ake ganin dan kasuwar nan marigayi Moshood Kashimawo Olawale Abiola na Jam’iyyar SDP ne ya lashe shi. A wannan tattaunawa Tofa wanda jigo ne Jam’iyyar APC ya ce bai kamata a ji tsoron tattauna batun ballewa daga kasar nan a wurin taron kasa ba:
Duk da soke-soke, Shugaba Jonathan ya kaddamar da taron kasa. Kana jin za a samu wani abin kirki daga taron?
Muna fata taron zai samar da wani abin kirki, sai dai daga farko kafin Shugaban kasa ya ce yana goyon bayansa kuma zai gudanar da shi, yana matukar kinsa, kwatsam sai ya sauya ra’ayi wanda hakan ne ya kawo shakku a zukatan jama’a da dama, wadanda suka rika tambayar ko Shugaban yana da wata muguwar manufa ce, shi ya sa taron ya zo dab da lokacin babban zabe. Wannanne dalilin da mutane da mutane da dama ba su goyon bayan taron, saboda suna da yakinin akwai daurin boye a cikinsa, mun dai zuba ido. Mutane da dama da suke halartar taron a baya suna sukarsa, to amma samun Naira miliyan hudu duk wata, da wahala ka ce mutane kada su je, saboda galibinsu sun yi ritaya ne suna neman abin yi.
Kamar yadda nake yi – sukar almubazzarancin gwamnati musamman wannan sata da majalisar dokokin kasa ke yi- idan aka zabe ni in je taron kan Naira miliyan hudu ba zan je ba, saboda hakan na nufin ni munafuki ne. Yana nufin a yayin da nake sukar wasu da sata da barnat dukiya, ni ma ga shi ina yin haka. Don haka mutane da dama da na sani suna sukar gwamnati kan barnar kudin jama’a sun je taron ne saboda kudin. Idan wani daga cikinsu zai je can amma ya ki karbar ko kwabo, sai dai ya halarci taron domin bukatun kasa, to ina jin zai zame gwarzona.To amma na san da yawansu za su je ne domin kudi. Kuma tunda zai gudana babu wanda zai iya hana shi, sai dai mu yi fatar a karshe alheri ya biyo bayansa.
Yallabai, lokacin kaddamar da taron Shugaban kasa ya lissafa sassan da wakilan za su kauce musu da wadanda za su tattauna. Me kake jin ya kamata a tattauna a taron?
Wannan taro ban a wakilan jama’a ba ne, ban a wadanda ’yan Najeriya suka zaba su wakilce su ba ne. Ban zabi wani ya je can ba; karamar hukumata ba ta zabi kowa ya je canba. Wannan taro ne na mutanen da aka zabe su domin wasu dalilai ko wasu mutane da suke goyon bayan gwamnati. A wurina duk abin da za a tattauna ba zai yi wani alfanu ba, tattaunawa ce da ba zata zama doka ba ko a aiwatar da ita, saboda ba su da iko. Masu ikon canja al’amura a kasar nan su ne Majalisar Dokoki ta kasa da majalisun dokoki na jihohi.
Na biyu, babu laifi ‘’yan Najeriya su zauna su tattauna batutuwa, saboda akwai bukatar su rika magana, koda tattaunawar ba za ta samu goyon bayan doka ba. Duk wani abin da ke damun Najeriya wajibi ne a tattauna shi ba tare da yin iyaka ba. Wasu daga cikin matsalolin kasar nan su ne an bar abubuwa da dama ba tare da tattaunawa kansu ba. Mun yi yaki ne saboda wani sashi na kasar nan bai son zama a kasar nan. Kuma har yanzu akwai mutanen da suke neman ballewa. Don haka a kyale mutane su bayyana fushinsu su fadi dalilin da ya sa suke son barin, ta yadda za mu ce: ‘a’a kada ku bari saboda dalilai kaza da kaza.’ Mu gamsar da kanmu cewa na farko muna son zama tare kuma akwai alfanu a cikin zamanmu tare kan wasu ka’idoji. Na rubuta littafi a 1986 da ake kira ‘Neman Hadin Kai’ wanda ba a buga shi ba, kuma n ace daya daga cikin matsalolinmu shi ne ba mu zama mu tattauna a kan wadanne ka’idoji ne muke son zama tare. Mene ne ya fi dacewa da kowane dan Najeriya kuma me suke bukata? Mu tsara wata yarjejeniya kana bin da ya sa muke son zama tare ta yadda za mu san akwai iyakokin da ba za mu tsallake ba, saboda muna da yarjejeniya. Amma yanzu muna zaune ne ba tare da wata yarjejeniya ba. Kuma tunda mun shekara 100 muna tare, akwai bukatar mu yanke shawara kan wasu abubuwa masu muhimmanci gare mu, lura da irin yadda muka yi zaman tare. Idan ka ce kada su tattauna haka to mene ne alfanun taron?
Shugaban kasar yana da ra’ayin cewa duk abin da zai iya kawo barazana ga hadin kan kasa bai kamata a tattauna shi ba.
Me yiwuwa saboda ana kallon wadannan sassa masu hadari ne. To amma duk wandana daukarsu masu hadari ne. Amma duk wanda ke son ballewa daga Najeriya a kyale su su balle su bar saura su zauna lafiya. Abin da na sani Arewa ba za ta taba cewa tana son barin Najeriya ba. Muna son zama cikin jin dadi da kowa a Najeriya saboda mu masu rungumar jama’a ne. Dubi misalin Kano, wata karamar Najeriya ce saboda kowace kabila tana da jama’a a Kano. Muna da kasa da zuciyar rungumar kowa. Wannan ne ya sa mutane daga Kudu suke jin dadin zama a nan. Sun gina gina gidajensu da coci-coci suna harkokin kasuwancinsu cikin ’yanci. Ba ma daukarsu a matsayin baki, muna daukarsu a matsayin ’yan uwanmu ne ’yan kasa. Don haka ra’ayina shi ne duk wanda yake son barin Najeriya a kyale su su bar mu, muna da abubuwan da za mu iya rayuwa da su. Akwai kasashen da suke da kasa da kashi daya na albarakatun da muke da su suna zaune cikin jin dadi. Amma nan muna da matsalolin gaban addini da na kabilanci, kuma ba mu son mu tattauna su. Me muke jin tsoro, alhali bai kamata mu ji tsoron tattauna matsalolinmu ba, saboda hanyar da kawai za mu ci gaba ita ce mu tattauna su a fili cikin gaskiya. …Na biyu wasu daga cikin gafalallun mutane a can suna maganar ballewa. Idan suka balle daga Najeriya ba za su taba zama cikin kwanciyar hankali ba, saboda suna zama ne irin na zuriya-zuriya kuma za su yi ta fada a tsakaninsu kan man fetur din. A karshe sai a rasa wanda zai je can ya sayi fetur din, saboda suna fama da fada a tsakanin zuriyoyi. Najeriya tana zaune lafiya saboda kowa yana jin ya fito ne daga kasa daya muna taimakon juna don a zauna lafiya. Duk wanda ya balle shi zai ji a jikinsa.
Akwai damuwa kan nuna wa Arewa halin bora wajen zaben wakilan taron, kuma wasu mutane na kiran a kaurace wa taron, bisa tunanin Arewa ba za ta iya gabatar da bukatunta ba. Me za ka ce kan haka?
Kun gani, muna da matsala tsakanin Arewa da Kudu, kuma wata matsalar ita ce wakilai Kiristoci sun fi Musulmi yawa. Wadannan su ne matsalolin da Shugaban kasa ya ce ba za taba su ba. Tun a zaben wakilai matsala ta bayyana amma an ce kada mu tattauna su. Wannan ne ya sa bai kamata a ce akwai batun da ba za a tabo ba, domin kauce wa matsaloli irin wadannan a taro na gaba. Mu tattauna komai ciki har da batun ballewa daga kasa da wasu fusatattun kungiyoyi ke yi, kamar masu neman Biyafara kai har da Boko Haram. Mu tambaye su me ya sa suke yin abubuwan da suke yi, domin mun san akwai korafe-korafe. Domin ko a lokacin yaki akan tattauna kuma galibi yake-yake na kawo karshe ne ta hanyar yarjejeniya. Hatta hadin kan kasar nan akwai bukatar a kulla yarjejeniya a kai, saboda ba za mu ci gaba da zama kan wannan yanayi na rashin yarda da juna ba. Wannan ya sa taron nan ba zai zama cikakke ba. A karshe ba za mu san me za mu yi da rahoton taron ba, saboda haramtacce ne. Hatta Majalisar Dokoki ta kasa da majalisun dokoki na jihohi ba za su aiwatar da shi ba, saboda akwai bukatar su tuntubi wadanda suka zabe su. Idan da Shugaban kasa yana da hikima da ya kafa kwamitin mutum 50 masu hangen nesa ya yi, su kawo rahotannin dukkan tarurrukan baya su daddale su, su fitar da rahoton da ya fi kyau su mika wa Majalisar Dokoki ta kasa. Wannan zai fi sauki da zama alheri. Babu wani sabon abu da za a tattauna, abin da kawai za a tattauna shi ne batun hadin kan kasar nan, wanda kuma sun ce ban da shi.
dabi’un Shugaba Jonathan suna nuna zai tsaya takara a badi, sabanin yarjejeniyar da ake takkadama ya cimma da gwamnoni a shekarar 2011. Me za ka ce kan haka?
Ra’ayina shi ne doka ta ba shi damar tsayawa takarar, don haka wajibi ne a bar shi ya tsaya takar ya alla kana sonsa ko a’a.
Wannan ’yancinsa ne na doka. Idan jam’iyyarsa ta ba shi wannan dama ta sake tsayawa takara to wane ne zai ce ba zai yi ba? Abin da ’yan Najeriya za su iya yi idan ba su sonsa shi ne su kada shi a zabe. daya daga cikin inda dimokuradiyyarmu ta gaza shi ne wannan batu na karba-karbar mulki a tsakanin Arewa da Kudu. Ina ganin wannan batu na Kudu da Arewa illa ne ga dimokuradiyya. Kowane mutum daga ko’ina yake a bar shi ya tsaya takara, sannan kuma a bar ’yan Najeriya su zabi wanda suke so.
A ra’ayina ina ganin ya kamata mu yi watsi da batun shiyya-shiyya mu kyale dimokuradiyya ta yi aikinta. A bar kowane dan Najeriya ya samu damar tsayawa takara, wannan ne ya sa nake fada wa Jam’iyyar APC cewa kada ta kebe kujerar Shugaban kasa ga Arewa ko Kudu. Duk mutumin da ke son tsayawa takara daga Kudu ko Arewa a zaben badi ya zo babban taron jam’iyya. A kyale ’ya’yan jam’iyya su zabi dan takararsu a babban taron jam’iyya. Idan suka yi haka, su gabatar da wannan dan takara ya alla daga Arewa ne ko Kudu mu tafi zabe. Amma idan ka ce, ‘dole ya fito daga Arewa,’ mutanen Kudu suka ce, ‘me za mu yi da wannan jam’iyya da ta riga ta yi waje da mu,’ wannan na iya illa ga APC wajen lashe zaben badi.
Akwai rahotannin da ke cewa ku mutanen APC kun riga ku ajiye mukamin ga Arewa, akwai mamaki da kake fadin haka.
Ba mu yi ba. Buhari yana da sha’awa, mai yiwuwa Okorocha yana da sha’awa, kila wani ma yana da sha’awa. Ni kuma na ce kada a hana su.’ Ta yiwu akwai mutum biyu ko uku daga Arewa da suke da sha’awa kuma za a iya samun wasu Yarabawa. A kyale dukkansu su tafi wurin babban taron jam’iyya, kuma a bar ’ya’yan jam’iyya su zaba daga cikinsu. Wannan ne hanyar da ta kamata a bi.