Bai kamata yunwa ta yi ajalin kowane yaro ba a Najeriya — Remi Tinubu
Sanata Tinubu ta kuma yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa jajircewar gwamnatinsa wajen bunƙasa fannin lafiya.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce bai kamata yunwa ko ƙarancin abinci su zama silar da za su yi ajalin kowane yaro ba a Najeriya.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bayyana haka ne a ranar Asabar yayin ziyarar aiki da ta kai Jigawa, inda ta ƙaddamar da Bankin Abinci na Ƙasa (National Food Bank Initiative), tare da wasu manyan ayyukan raya ƙasa.
- An maka Tinubu a kotu ana neman hana shi takara a Zaɓen 2027
- Amurka ta ƙara yawan tallafin da za ta ba Venezuela zuwa dala miliyan 300
A yayin ziyarar, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Oluremi Tinubu Clinics da aka gina a garin Hadejia, tare da tallafin Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa.
Ta bayyana cewa gina asibitin wata babbar gudummawa ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya musamman ga al’ummar karkara, tana mai cewa za a samu sauƙin samun ingantattun ayyukan jinya ga dubban mazauna Hadejia da maƙwabtan yankin.
Sanata Oluremi Tinubu ta ce ta ji daɗin yadda aka sanya wa asibitin sunanta, tana mai bayyana hakan a matsayin babban abin girmamawa gare ta.
“Mun zo ne domin ƙaddamar da wannan cibiyar lafiya da ɗaya daga cikin fitattun ’ya’yan wannan yanki ya samar ta hanyar haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki. Na yi matuƙar godiya da aka sanya wa asibitin sunana,” in ji ta.
Ta kuma yaba wa al’ummar Hadejia saboda yadda suke samar da mutane masu bayar da gudummawa ga ci gaban ƙasa ta hanyar aiwatar da ayyukan al’umma masu amfani.
Game da shirin Bankin Abinci na Ƙasa, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce an ƙirƙiro shi ne domin magance matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da ke addabar mata masu juna biyu, masu shayarwa da kuma yara ’yan ƙasa da shekara shida.
Ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya umurce ta da ta jagoranci ƙoƙarin da zai taimaka wajen rage matsalar rashin wadataccen abinci mai gina jiki a faɗin ƙasar nan.
A cewarta, maimakon jiran yara su kamu da matsananciyar tamowa, shirin zai mayar da hankali wajen hana matsalar tun farko ta hanyar bai wa mata masu juna biyu da masu shayarwa, da kuma ƙananan yara, abinci mai gina jiki.
Ta bayyana cewa za a kafa cibiyoyin Bankin Abinci a kusa da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko domin sauƙaƙa wa masu cin gajiyar shirin samun abinci mai gina jiki yayin karɓar kulawar lafiya.
Sanata Tinubu ta ce shirin ya samu gagarumar goyon baya daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Ta bayyana cewa Kamfanin Dangote ya bayar da tallafin kayan abinci na Naira biliyan 20, yayin da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL ke ɗaukar nauyin gina cibiyoyin Bankin Abinci a faɗin ƙasa kan kuɗin Naira biliyan 30.
Ta kuma bayyana cewa ita da kanta ta bayar da gudummawar Naira miliyan 500 ga shirin, yayin da wasu kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane ke ci gaba da bayar da tallafi.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta yaba wa gwamnonin yankin Arewa maso Yamma saboda haɗin kan da suke bayarwa, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen samun nasarar aiwatar da shirin.
Har ila yau, ta yaba wa Uwargidan Gwamnan Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi, bisa irin gudummawar da take bayarwa wajen aiwatar da shirin sabunta fata na gwamnatin Tinubu da ake yi wa laƙabi da Renewed Hope Initiative a jihar.
“Na ji daɗin yin aiki tare da ita. Duk lokacin da aka buƙace ta tana kasancewa a shirye. Ta yi gagarumin aiki wajen bunƙasa shirin Renewed Hope a Jigawa,” in ji ta.
Sanata Tinubu ta kuma yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa jajircewar gwamnatinsa wajen bunƙasa fannin lafiya, inganta abinci mai gina jiki da kuma aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.
A yayin ziyarar, Remi ta ƙaddamar da titin Hadejia zuwa Garun Gabas, da titin Remi Tinubu da ke Gandun Sarki, sannan ta kai ziyara Cibiyar FutureMap ta NITDA da ke kan hanyar Nguru, ta duba Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko da ke Gandun Sarki, tare da buɗe Cibiyar Bankin Abinci ta Ƙasa.
Taron ya samu halartar Gwamnan Jigawa, Malam Umar A. Namadi, da mai ɗakinsa Hajiya Hadiza Umar Namadi, gwamnoni daga jihohin Arewa maso Yamma, ministoci da matansu, sarakunan gargajiya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Hadejia, da manyan jami’an gwamnati da kuma abokan hulɗar ci gaba.
Ana sa ran bayan ƙaddamar da Asibitin Oluremi Tinubu Clinics da kuma fara aikin Bankin Abinci na Ƙasa zai ƙara inganta samun ingantaccen kiwon lafiya da abinci mai gina jiki, tare da rage mace-macen mata masu juna biyu da ƙananan yara a Jihar Jigawa.