Bai wa matasa ragamar shugabanci ba shi ne mafita a Najeriya ba – Iliya Musa
Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) na Kudancin Kaduna, Alhaji Iliyasu Musa ya ce bai wa matasa shugabancin kasar nan, ba shi ne mafita ga halin da kasar ta tsinci kanta a ciki ba, bilhasali ma hakan sai dai ya kara jefa kasar cikin wata matsala ta daban. Sakataren ya bayyana haka ne a yayin […]

Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) na Kudancin Kaduna, Alhaji Iliyasu Musa ya ce bai wa matasa shugabancin kasar nan, ba shi ne mafita ga halin da kasar ta tsinci kanta a ciki ba, bilhasali ma hakan sai dai ya kara jefa kasar cikin wata matsala ta daban.
Sakataren ya bayyana haka ne a yayin tattaunawarsa da Aminiya a makon jiya. Alhaji Ilyasu ya ce akwai matukar hadari ga mutumin da bai gama mallakar hankalinsa ba, a ce za a dauki mulkin jama’a a damka masa.
“Babu wani matashi da zai fito neman wani matsayi ko mukami face ya bukaci wani babba da zai tsaya masa wajen dawainiyar kashe kudin zirga-zirgar yakin nema kuri’a da sauransu. Don haka a ganina ko da an bai wa matasa ragamar shugabanci, zai zamo canjin salo ne kawai na ci gaban mulkin tsofaffin da aka guda, domin kowa zai cusa nasa ne,” inji shi.
Da ya waiwayo kan salon da wadansu daga cikin sarakunan yankin Kudancin Kaduna ke yi na bai wa matasa ragamar yin magana da yawunsu tattare da cewa akwai sarakuna da dattawa da kuma malamai amma sai su nuna wani su ce shi ne shugaban matasa, shi zai yi magana a madadinsu da sauran jama’ar gari gaba daya, ya ce hakan zubar da kimar sarauta ce da kuma nuna dattawansu ba a bakin komai suke ba. A cewarsa, idan har ba za su iya tsawatarwa da kuma yin magana a madadin jama’arsu ba, to kamata ya yi su tube rawunnansu su nada wa matasan.
Alhaji Iliya, wanda har ila yau shi ne Shugaban kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya ta Community Peace Partnership, (CPP) na karamar Hukumar Jama’a, ya ce in dai har za su yi mulki tsakaninsu da Allah, to ya kamata su taimaka wa gwamnati ne wajen kokarin samar da zaman lafiya.