Bai wa qananan hukumomi ‘yanci zai raya yankunan karkara – Chindo Gona

Wani dan siyasa kuma dan takarar shugabancin Qaramar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato a qarqashin Jam’iyyar APC, Honorabul Chindo Gona ya bayyana cewa bai wa qananan hukumomin qasar nan ’yanci, zai ba da dama a yi wa al’ummar da suke zaune a yankunan karkara ayyukan raya qasa.  Honorabul Gona, ya bayyana haka ne a […]

Bai wa qananan hukumomi ‘yanci zai raya yankunan karkara – Chindo Gona

Wani dan siyasa kuma dan takarar shugabancin Qaramar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato a qarqashin Jam’iyyar APC, Honorabul Chindo Gona ya bayyana cewa bai wa qananan hukumomin qasar nan ’yanci, zai ba da dama a yi wa al’ummar da suke zaune a yankunan karkara ayyukan raya qasa. 

Honorabul Gona, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a wannan mako, yana mai cewa babu shakka dokar bai wa qananan hukumomi ’yanci da ake qoqarin yi wa gyara, doka ce mai qarfi wadda za ta bai wa qananan hukumomi damar bunqasa, kuma hakan zai taimaka wa al’ummar qasar nan. “Domin idan aka duba Gwamnatin Tarayya wata gwamnati ce mai zaman kanta, haka gwamnatin jiha, sannan da gwamnati qaramar hukuma, wadda a nan ne talakawa suke zaune.”

Ya ce don haka Shugaban Qasa, Muhammadu Buhari yake qoqarin ganin an bai wa qananan hukumomin qasar nan ’yancin cin gashin kansu, don samun damar yi wa al’umma’ar karkara ayyukan raya qasa.

Honorabul Chindo Gona ya yi kira ga ’yan majalisa da suke jihohin Najeriya su yi qoqari su amince da wannan doka, domin taimaka wa al’ummar qasar nan, musamman mazauna yankunan karkara. “Allah ne Yake bayar da shugabanci ga wanda Ya so. Don haka ina kira ga al’ummar Jihar Filato su fito su zabi shugabannin da suke so, a wannan zabe na qananan hukumomi da za a gudanar a jihar. Kuma a yi wannan zabe a cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tashin hankali ba,” inji shi.