‘Bai yiwuwa a auna nasarar gwamnati a cikin kwanaki 100’
A gobe ne Shugaba Muhammadu Buhari zai cika kwanaki 100 a kan karagar mulkin kasar nan, sai dai kuma al’amarin ya jawo cece-ku-ce a tsakanin al’ummar kasar nan, inda wadansu suke ganin a cikin wadannan kwanakin shugaba Buhari ya fara saka da farin zare, domin ya gudanar da abubuwa da dama da za a yaba, […]

A gobe ne Shugaba Muhammadu Buhari zai cika kwanaki 100 a kan karagar mulkin kasar nan, sai dai kuma al’amarin ya jawo cece-ku-ce a tsakanin al’ummar kasar nan, inda wadansu suke ganin a cikin wadannan kwanakin shugaba Buhari ya fara saka da farin zare, domin ya gudanar da abubuwa da dama da za a yaba, a yayin da wadansu kuma suke ganin babu wani abun a-zo-a-gani da shugaban ya gudanar zuwa yanzu.
Jam’iyyar adawa ta PDP na sahun gaba wajen sukar salon mulkin Buhari, inda take ganin ya mayar da hankalinsa ne kawai wajen muzanta gwamnatin Jonathan da ta gabata.
Kodayake tun kafin a zabi shugaba Buhari ya bayyana wa ‘yan Najeriya a wani taro da suka yi da shi a kasar Ingila cewa shi bai yarda da tsarin gwada takun sabuwar gwamnati a cikin kwanaki 100 ba, domin a ganinsa wannan wata hanya ce kawai ta yaudara, saboda ba zai yiwu a gudanar da muhimman abubuwa a cikin kwanaki 100 da kafuwar gwamnati ba.
Shi ma mai taimaka wa shugaban ta fuskar yada labarai Malam Garba Shehu ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa shugaba Buhari ya taba yin alkawarin gudanar da wadansu muhimman ayyuka a cikin kwanaki 100 idan aka zabe shi, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da wannan batun.
Da Aminiya ta tuntubi shugaban kungiyar kare muradun Arewa (ACF) Alhaji Ibrahim Commasie, cewa ya yi, ‘’Kwanaki 100 sun yi kadan a auna gwamnatinsa, ni bana cikn masu cewa da mutum ya kama aiki, ko an zabe shi a fara maganar wai ya kamata a ga aiki cikin kwanak 100, musamman a ji wai ko ya yi kokari ko bai yi ba. Najeriya ce fa kuma babbar kasa ce. Amma duk da haka an yi kokari, domin an samu cigaba kwarai da gaske. Da farko dai a yanzu ma’aikata ko’ina suke suna tsoro saboda sun san wanda ke kan gadon mulki ba mai wasa ba ne. Saboda haka duk wanda ya zalunci kasa ko ya ci kudi za a kamo shi.
Na biyu kuma akwai babban cigaba da aka samu wajen yaki da ‘yan Boko Haram don abubuwa sun canza, kodayake suna yin ta’asa, amma har yanzu ana farautarsu, an kuma kai su makura domin gamawa da su. Ai wannan shi ma cigaba ne. Ya Kuma fara nade-naden mukaman da suka kamata, kamar na su masu tsaron kasa, irin su Hafsoshin soja na sama da na kasa da sauransu. Duk wadannan nade-nade da ya yi ai daidai ne.’’
Dangane da ko shugaba Buhari ya nuna a aikace batun nan da ya yi cewa shi ba na wani ba ne, na kowa ne, Sai shugaban na ACF ya ce,’’Ya nuna mana, domin babu wanda zai zo ya rika juya shi. idan ya yi bincike zai dauki mataki a kan ko wane ne ya aikata laifi, ba tare da wani ya je yana fada masa abin da zai yi ba. A’a duk wani nade-nade da ya yi sai da ya bincika da kansa bayan ya gamsu sannan ya yi nazari tare da samun cikekken bayanai a kan mutum sannan ya nada shi. uDk abin da yake yi ya nuna da gaske yake yi ba wasa ba.’’
Shi kuwa tsohon dan takarar shugabasn kasa a karkashin inuwar tsohuwar jam’iyyar PRP Khalifa Hassan Yusuf da ke Damaturu jihar Yobe cewa ya yi, nasarorin da Buhari ya samu a kwanaki 100 sun fi wadanda gwamnatin tsohon shugaba Jonathan ta cim ma a tsawon shekaru 6.
Ya ce, kasancewar shi shugaban kasa Buhari mutum ne da ya kware a kan sha’anin gudanar da mulki shi ya sa tun farko ya fara da cika alkawarin da ya yi bankado masu taurin bashi da kuma ba da dama ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su kwato dukiyoyin al’umma ba tare da ya taka musu birki ba, sabanin a baya da idan mutum shafaffe da mai ne ba ya laifi ballantana a kama shi.
Ya ci gaba da cewa, ‘idan aka duba irin sababbin nade-naden da shugaban kasa ya yi za a ga cewa bisa cancanta ya yi, domim dukanin mutanen da ya nada sun dace da matsayin da aka ba su.
Khalifa Hassan ya kara da cewa, ‘’a yanzu idan aka duba matakan da shugaban kasa ya dauka a ‘yan kwanakin da ya yi, musamman kan harkokin Boko Haram da ya tsaya a makogoron al’ummomin yankin Arewa maso gabas, da ma kasa baki daya, matsalar da gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan ta gaza shawo kanta, da kuma matsalar wutar lantarki da shi ma a baya lamarin ya gagari kwandila, amma cikin kankanin lokaci sabon shugaban kasa ya dauki matakin kawo karshensu.’’
‘’Don haka mu yanzu fatanmu ga Muhammadu Buhari shi ne Allah (SWT) Ya ba shi damar ci gaba da ayyukan nan na alheri da ya fara. Kuma ina ba shi shawarar ya rika gauraya ko’ina, wato daga sama har kasa a yayin gudanar da ayyukansa.’’
Dangane da zargin da bangaren Kudu maso gabashin Nijeriya ke yi cewa ba a ba su wani mukami ba, sai ya ce, ‘sun yi gaggawa, tunda wadannan sababbin nade-nade tamfar yanzu aka fara, kuma ma ai koda Buharin ya yi hakan bai yi laifi ba, domin ai da abokin daka ake shan gari.’’
Shi kuwa Sulaiman Hashim, matashin da ya yi tattaki daga Legas zuwa Abuja da kafa don murnar nasarar Buhari a lokacin zabe, ya yaba da nasarar samar da tsaro da gwamnatin Buharin ta cim ma ne, sai dai ya ce gyara sauran barnar da gwamnatin ta tarar zai dauki lokaci. Ya ce shugaban kasa ya kwashe mafi yawan wata uku da ya yi a kan mulki wajen fuskantar bangaren tsaro, wanda ya ce sai da shi ne za a samar da wani ci gaba.
A game da tattakin da ya yi kuwa, Sulaiman ya ce al’amarin ya jawo masa daukaka, sai dai ya ce bai amince da kiran da wadanda su ka kwaikwayi abin da ya yi ba na su kafa kungiyarsu, inda ya ce tafiyar da ya yi na cika alkawari ne da ya yi tun gabanin nasarar, sabanin na takwarorin nasa, da ya ce tafiyarsu ta takaita a kan murna ne kawai.