Ba’Indiye ya aurar da matarsa ga kanensa

Wani Ba’indiye a Jihar Bihar da ke kasar Indiya ya aura wa kanensa matarsa bayan sun damfaru da kaunar juna, kamar yadda jami’an hukuma da ’yan uwan ma’auratan suka bayyana ranar Juma’ar makon jiya. Kuma ya danka musu ’yarsa ’yar shekara biyu, inda ya bukaci ango da amarya su kula da ita,  daga bisani ya […]

Ba’Indiye ya aurar da matarsa ga kanensa

Wani Ba’indiye a Jihar Bihar da ke kasar Indiya ya aura wa kanensa matarsa bayan sun damfaru da kaunar juna, kamar yadda jami’an hukuma da ’yan uwan ma’auratan suka bayyana ranar Juma’ar makon jiya.

Kuma ya danka musu ’yarsa ’yar shekara biyu, inda ya bukaci ango da amarya su kula da ita,  daga bisani ya yi bankwana da kauyensu, zuwa wani wurin da ba a sani ba, kamar yadda wanda lamarin ya auku a gabansa ya bayyana.

Wannan al’amari dai ya auku ne a kauyen Ghogha da ke gundumar Bhagalpur kimanin kilomita 250 daga Patna a Jihar Bihar. Kuma shi ne al’amari irinsa na farko da ya taba aukuwa don haka ake ta labarinsa ko’ina a garin.

Rahotanni sun nuna cewa Pawan Goswani mai shekara 30 ya auri Priyanka shekara hudu da suka wuce. Ma’auaratan sun kasance cikin kwanciyar hankali da annashuwa tare da ’yarsu.

Rayuwa ta yi musu mummunan sauyi ne a shekaru biyun bayan nan lokacin da Priyanka ta ji cewa ta damfaru da soyayyar kanen Pawan mai suna Sajan, har suka yi kudurin auren juna ko ana ha maza, ha mata.

Da farko iyayensu sun yi kokarin shawo kansu kan su sake tunani game da wannan aure.

Kwatsam sai Pawan ya amince da auren, inda ya saki matarsa, ya shirya bikin aurar da matarsa ga kanensa.

Priyanka da Sajan sun yi aurensu a wani dakin ibadar Hindu a gaban dimbin al’ummmar kauyensu. Kuma masu gudanar da harkokin dakin ibadar sun bayar da shaida ga wadannan sababbin ma’aurata, al’amarin da ya tabbatar da su a matsayin ma’aurata.

“ba na son damalmala farin cikinsu, don haka na yanke matsayar yi musu aure. Ina cike da farin ciki matata yanzu tana cikin farin ciki, tare da kanena,” kamar yadda Pawan ya bayyana wa jaridar Gulf News a hirar da suka yi ta wayar tarho ranar Juma’ar da ta gabata.

Kuma ya danka musu ’yarsa ’yar shekara biyu, inda ya bukaci su kula da ita bayan ya tafi abinsa.

Pawan dai ya tafi abinsa yana zubar da hawaye a bainar jama’a., inda mutanen kauyen suka yi ta kokarin kwantar masa da hankali, suka kuma roke shi kan ya rika ziyartar kauyen.

Wannan aure da aka gudanar a karshen makon da wuce a Bihar an yi kwatankwacin abin da ya faru a jihar, inda wani matashi dan shekara sha wani abu ya rataye kansa, bayan da kotu ta shirya aurensa da matar wansa da ya mutu, wadda ya dauke ta tamkar uwa. An yi bikin auren ranar Litinin din da ta wuce, amma ya kashe kansa ne da yammaci, saboda bakinsa game da auren.