Ba’indiye ya kunna wa kansa wuta ya rungumi dan siyasa
Wani Ba’indiye da ’yan sanda suka bayyana sunansa da Durgesh Kumar Singh, ya fito daga cikin ’yan kallon taron siyasa, inda ya watsa wa kansa fetur, ya kunna wuta sannan ya rungumi shugaban Jam’iyyar Bahujan Samaj Party (BSP ) , Kamruzzama Fauji. Gidan talabijin na Tb Doordarshan da ke Lucknow a kasar Indiya, ya nuna […]
Wani Ba’indiye da ’yan sanda suka bayyana sunansa da Durgesh Kumar Singh, ya fito daga cikin ’yan kallon taron siyasa, inda ya watsa wa kansa fetur, ya kunna wuta sannan ya rungumi shugaban Jam’iyyar Bahujan Samaj Party (BSP ) , Kamruzzama Fauji. Gidan talabijin na Tb Doordarshan da ke Lucknow a kasar Indiya, ya nuna hoton mutane a lokacin da suke kokarin ceton rayukansu.
Wannan mummunan lamari ya auku ne a lokacin da tashar talabijin din ke nuna muhawarar ’yan takara a garin Sultanpur da ke kimanin kilomita 160 daga Lucknow.
“Wannan mutumin ya fito ne kwai sai ya watsa wa kansa fetur, ya kunna wa kansa wuta, sannan ya rungumi wani daga cikin bakin manyan ’yan siyasa, ya rike gam,” a cewar wani mai daukar hoto, Pankaj Kumar Gupta.
“Mutanen sun yi matukar shiga cikin damuwa ganin wannan al’amari da ya auku,” inji wannan mai hoto, da hotunansa suka nuna mutanen biyu suna cin wuta
Wasu ’yan siyasa biyu da suka halarci shirin talabijin din, wato Ram Kumar Singh da Chowdhary Hriday Ram berma, duk sun samu raunuka. A daidai lokacin da suke okarin cetar dan uwansu.
Har yanzu daidai ba a gano dalilin aikata wannan mummunan abu ba. Gidajen talabijin a kasar Indiya sun saba shiryamuhawarar dare a daidai lokacin da ake gudanar da zabukan higa majlisar kasar.