Ba’indiye ya sanya rigar zinari mai nauyin kilo hudu

Wani Ba’indiye, mai suna Pankaj Parakh, wanda ya kasa kammala makaranta, har aka kore shi, ya tara dimbin dukiya a harkar sayar da tufafi, har ta kai ga ya mallaki rigar zinari mai nauyin kilo hudu, wadda aka kimanta kudinta a matsayin Dala dubu 214 (Naira miliyan 35,310000).Ba’indiyen ya yi suna a titin Yeola da […]

Ba’indiye ya sanya rigar zinari mai nauyin kilo hudu
Ba’indiye ya sanya rigar zinari mai nauyin kilo hudu

Wani Ba’indiye, mai suna Pankaj Parakh, wanda ya kasa kammala makaranta, har aka kore shi, ya tara dimbin dukiya a harkar sayar da tufafi, har ta kai ga ya mallaki rigar zinari mai nauyin kilo hudu, wadda aka kimanta kudinta a matsayin Dala dubu 214 (Naira miliyan 35,310000).
Ba’indiyen ya yi suna a titin Yeola da ke kilomita 260 daga birnin Mumbai, inda mata da maze ke rurubibin kallonsa, a duk lokacin da ya sanya abin wuya na kawa mai nauyi kilo uku.
Da ranar haihuwarsa ta zagayo, a karo na 45, wato yasu Juma’a, ya sanya an yi masa rigar zinari, wadda ya sanya a wurin wani taro da manyan mutane suka halarta, hard a ministan Yawon Bude ido, Mahastara da Chhaga Bhujbal na Jam’iyyr NCP da sauran ’yan majalisa ke wakiltar al’umma a jam’iyyu daban-daban na kasar Indiya.
Wannan riga ta shi, mai maballai bakwai duk na zinariya, ana ganin Parakh zai shiga kundin tarihi na Guiness Book of Record da Limca Books of Record.
Wannan riga dai Kamfanin Bafna Jewellers da ke Nashik da Shanti Jewellers ne suka shafe wata biyu suna kera masa ita, inda kimanin kwararru 20, suka shafe sa’o’i dubu uku da mintuna 200 suna aikin dinkata.