Ba’indiye ya shafe shekara 48 yana aiki a kamfani guda

Wani Ba’ mindiye da ya shiga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), shekaru uku gabanin a kafa kasar, ya yi aiki na tsawon shekara 48, kuma ya shafe shekara 38 a matsayi guda a wani kamfani. Mutumin mai suna A.A. Salami shi ne mutum na biyu a duniya da ya dade a aiki a wuri daya, mutum […]

Ba’indiye ya shafe shekara 48 yana aiki a kamfani guda
Ba’indiye ya shafe shekara 48 yana aiki a kamfani guda

Wani Ba’ mindiye da ya shiga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), shekaru uku gabanin a kafa kasar, ya yi aiki na tsawon shekara 48, kuma ya shafe shekara 38 a matsayi guda a wani kamfani. Mutumin mai suna A.A. Salami shi ne mutum na biyu a duniya da ya dade a aiki a wuri daya, mutum mafi dadewa a aiki da aka taba ruwaito a littafin fitattun al’amura na Guinness World Book of Record, an ce ya shafe shekara 80 ne yana aiki a wata masana’antar kere-kere da ke Amurka, mai suna Thomas Stoddard.
A.A. Salam mai shekara 74 ya shafe 48 yana aiki a kamfanin safarar jiragen sama na Omeir Trabel Agency da ke Abu Dhabi.
Sabanin sauran bakin da ke kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa, Salam, masanin kimiyya ne da ya kammala karatunsa a Kwalejin Farook da ke birnin Kerala ta kasar Indiya. Ya kuma yi aiki na tsawon shekara hudu a gidan waya da sashin kula da lafiya na birnin Bombay, kafin ya yi kaura zuwa kasar a ranar 2 ga Janairun 1968.
“Wani abokina ne ya taimake ni na samu bizar shiga kasar daga wannan kamfanin. Saboda bizata, ba na cikin jerin bakin masu aikin kwadago da ke shiga kasar a wancan zamani ba bisa ka’ida ba, inda suke hawa karamin jirgin ruwa,” A.A. Salam ya bayyana wa jaridar Khaleej Times.
Ya taso daga birnin Bombay zuwa Dubai a jirgin ruwa mai  suna Dumra. “Mun dauki kwana 10 kafin mu iso Dubai. Jirgin ya tsaya a tasharsa, inda aka rika sauke mu daya bayan daya. Washegari muka isa Abu Dhabi a cikin a kori-kura.Lokacin da na fara aiki, mu 17 ne a kamfanin. Muna kula da ayyuka ne a kananan filayen jiragen sama a Abu Dhabi, har zuwa lokacin da hukumar kula da hada-hadar filayen jiragen sama ta Abu Dhabi ta karbe su a 1976,” inji shi.
A cewarsa: “Kamfanonin safarar jiragen sama uku ne ko hudu kacal da bankuna hudu. Yanzu kuwa akwai daruruwansu. Domin kamfaninmu kadai yana da rassa 56 da ma’aikata 700. Da na fara aiki  a matsayin mai karbar kudi, ana biyana Dinari 70 na kudin Bahrain a matsayin albashi, haka na yi ta samun daukaka har na kai matsayin manaja mai kula da ma’aikata na kamfanin. Sai dai na rike mukami guda har na tsawon shekara 38. Ofishina na daya daga cikin manyan gine-gine da ke birnin. Gidajenmu kuwa na bulo ne. Kudin hayarmu kuwa Dinari 20 ne kowane daki. Ba mu da na’urar sanyaya daki. Babu tsayayyar wutar lantarki, kuma da safe kawai muke samun ruwan famfo.”
Ya kara da cewa “A lokacin da nake matsayin mai karbar kudi, sai na rika zuwa birnin Al Ain don karbo abin da aka tara na kowane wata. A zamanin babu mikakkiyar hanya, saboda haka sai mu hau kananan jiragen sama zuwa Al Ain. A wata shekara na fara ganin titin mota mai kwalta. Domin manyan ma’aikatan gwamnati ne da Shaikh suka mallaki motoci. Babu kasuwani da otal-otal. Wasu ’yan tsiraru ne ke samar da abinci. Wadanda ba su da aikin yi za su samu abin da za su ci a bashi, har sai sun samu aiki su biya. Shagunan dinki biyu da na kayan masarufi da aka kafa a lokacin, sukan ba mu bashi idan za mu tafi gida hutu. Kuma za mu biya su ne kawai idan mun dawo.”
 A 1969 ne Salam ya kawo matarsa. “daukacin ’ya’yana duk a nan aka haife su. Kuma a lokacin Indiyawa kadan ne ke tare da iyalansu. Don haka wadanda ke zaune a wurin sun san juna kwarai da gaske.
Babban dansa likitan idanu ne, wanda ya koma birnin Kerala shekara hudu da suka wuce. Shi kuwa mai bi masa kwararre ne a harkar hada-hadar kasuwanci a kasar Kanada
Salam na zaune ne tare da matar da ya sake aure bayan matarsa ta rasu a shekarar 2007.
Ya ajiye aiki ne don kashin kansa. Kuma ya yi nuni da cewa, bai taba tunanin neman wani aiki ba, duk tsawon wadannan shekaru. Kuma yana shirin komawa gida, inda zai rika gudanar da ayyukan jinkan al’umma a Kerala. Ya kuma gode wa hukumar gudanarwar kamfanin da suka tallafa masa tsawon wadannan shekaru da ya shafe yana aiki.