Ba’indiyen da ya shafe shekara 25 yana tafiya da baya ya manta tafiya ta gaba
Wani mutum a kasar Indiya da ya saba tafiya da baya da baya, har tsawon shekara 25, ya manta yadda ake tafiya ta gaba. Mutumin mai suna Mani Manithan, ya yanke wa kansa wannan tsarin rayuwa na tafiya dabaya, da baya ne a shekarar 1989, bayan da ya tsorata da tashe-tashen hankula da ake yawan […]
Wani mutum a kasar Indiya da ya saba tafiya da baya da baya, har tsawon shekara 25, ya manta yadda ake tafiya ta gaba. Mutumin mai suna Mani Manithan, ya yanke wa kansa wannan tsarin rayuwa na tafiya dabaya, da baya ne a shekarar 1989, bayan da ya tsorata da tashe-tashen hankula da ake yawan yi a tsakanin kabilun Indiya. Kuma manufarsa ita ce kawo zaman lafiya a daukacin fadin duniya.
Ya ce, wannan birkitaccciyar tafiya ba ta haifar da wata matsala ga rayuwarsa ta yau da kullum ba, domin ya kware da tafiya ta baya da hawa bene da tsallaka titunan, har ma a lokacin da yake hawan motar haya.
Sai dai wata matsalar da samu Mani, mai aiki kantin sayar da wayoyin hannu, a gundumar Tiruppatur da ke Tamil Nadu, ita ce ya manta yadda ake tafiya ta gaba.
“Yin tafiya yadda aka saba kalubale ne gareni, domin a tsarin tunanina na manta yadda ake yi. Domin na fi samun natsuwa da irin tafiyar da nike yi. Rayuwata cike take da fafutika da sadaukar da kai da samun nasarori da kuma zanga-zanga, don haka ba ni da wata matsala in na ci gaba da tafiya dabaya, da baya, har sai an tabbatar da zaman lafiya a duniya,” inji shi.
A lokacin da ya ci alwashin fara tafiya da baya, da baya, sai da ya shafe kilomita 350 yana tafiya daga garinsu zuwa birnin Chennai.
“Kuna dai ganin yadda ake ta ci gaba da ayyukan ta’addanci a duniya. Akwai yawan fashewar bama-bamai, kuma matasa na samun gurbatacciyar tarbiyya. Don in yi tur da wadannan al’amura, shi yasa nake tafiya da baya har na tsawon shekara 25. Manufata kawai, ita ce tabbatar da zaman lafiya a duniya,” inji shi.