Ba’indiyen da ya shekara 22 ba wanka
Fahimtar addini ce ta sa na daina wanka
Wani mai shekara 62 a yankin Bihar na kasar Indiya yana ta samun martani daga jama’ar kasarsa bayan da aka bayyana cewa, ya shafe shekara 22 bai yi wanka ba.
Mutumin mai suna Dharamdev Ram, wanda ya shahara a kauyensa na Baikunthpur, kowa ya san cewa ba ya wanka ko ba ya wanke wani bangare na jikinsa a cikin shekara 22.
- Ma’aikatan ganyen shayi 150,000 sun tsunduma yajin aiki a Bangladesh
- Ango ya fasa auren amaryarsa ana tsaka da biki saboda gajartarta
Sai dai babu wanda yake yi masa ba’a ko zolaya kan abin da ya yi, maimakon haka, yana samun girmamawa sosai kan shawarar da ya yanke wa kansa.
Hakan ya faru ne saboda ya sha alwashin ba zai yi wanka ba har sai an daina cin zarafin mata tare da magance rigingimun filaye a tsakanin maza da kuma kashe dabbobin da ba su ji ba ba su gani ba.
Har yanzu hakan bai faru ba don haka Dharamdev ya ci gaba da tsare alkawarinsa.
“A 1975, na yi aiki a wata masana’anta a garin Jagdal da ke Jihar Bengal, kuma na yi aure a 1978 kuma ina gudanar da rayuwata yadda ta dace,” kamar yadda Dharamdev Ram ya shaida wa kafar ETV Bharat.
“Amma a 1987, kwatsam na gane cewa rigingimun filaye da kashe-kashen dabbobi da cin zarafin mata sun fara karuwa.
“Don haka, ina neman amsa sai na tunkari wani masanin addini ‘Guru’ wanda ya dauke ni a matsayin almajirinsa, ya kwadaitar da ni ga bin tafarkin ibada.
“Tun daga nan, na hau tafarkin ibada na fara yin zurfin tunani ga abin bautana Rama.”
A shekarar 2000, lokacin da ya sha alwashin ba zai yi wanka ba sai abubuwan da ya ambata a baya sun daina aiki, Ram ya bar aiki a masana’antar da yake aiki, amma da sauri ya dawo saboda matsi daga iyalinsa.
Duk da haka, lokacin da aka yaga rahoton matakin da ya gauka game da alkawarinsa na sabon abu an kore shi, kuma ya kasance ba ya da aikin yi tun daga lokacin.
Matar Ram, mai suna Maya Debi, ta rasu a shekara ta 2003, amma duk da haka, ya ki yin wanka.
Shekaru da yawa bayan haka, gaya daga cikin ’ya’yansa ya rasu amma bai karya alkawarinsa ba kuma ya ci gaba da yin haka duk da cewa, gansa ya rasu a wannan shekara.
Ko da ma yana nufin ba zai taba yin wanka ba har sai ranar da ya rasu, tsohon mai shekara 62 a shirye yake ya cika alkawarin da ya yi shekara 22 da suka wuce, sai dai in ya cim ma burinsa.
Kokarin da Dharamdev Ram ya yi na kawo karshen cin zarafin mata da dabbobi da kuma takaddamar filaye ya yi kamari a Indiya kwanan nan, wanda ya haifar da wani bincike a jarida.
’Yan jarida sun yi tattaki zuwa Baikunthpur a Gundumar Gopalganj ta Bihar don yin hira da Ram da wasu mazauna yankin, wadanda dukkansu sun tabbatar da cewa bai yi wanka ba sama da shekara 20.
Idan kuna tunanin shekara 22, ba tare da wanka ba shi ne lokaci mai tsawo, “To tabbas ba ku taba jin labarin mutumin da ya fi kazanta a duniya ba, wani gan kasar Iran mai shekara 87 wanda bai yi wanka ba a cikin shekara 67.