Baiwa ce ta sa idan zan yi waka ba sai na rubuta ta ba —Naziru Gwauro

Za mu so ka gabatar da kanka?Sunana Naziru M. Adam amma mutane sun fi kira na da Naziru Gwauro. Dalilin da ya sa ake kira na Naziru Gwauro shi ne, akwai lokacin da muka taso daga Kano muka tare a Jihar Kaduna saboda matsalar da aka samu a harkar fim a Kano. A lokacin da […]

Baiwa ce ta sa idan zan yi waka ba sai na rubuta ta ba —Naziru Gwauro

Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Naziru M. Adam amma mutane sun fi kira na da Naziru Gwauro. Dalilin da ya sa ake kira na Naziru Gwauro shi ne, akwai lokacin da muka taso daga Kano muka tare a Jihar Kaduna saboda matsalar da aka samu a harkar fim a Kano. A lokacin da muka zo Kaduna daf da lokacin azumi ne. To dama an shirya wata waka da za a yi kan Gwauraye, sai aka ce ai babu wanda ya cancanci ya yi wannan wakar sai Naziru tun da shi ma yana cikin gwauraye. Saboda haka lokacin ni da Umar Sharrif muna Kaduna.
Mene ne takaitaccen tarihinka?
Ni dai an haife ni a Jihar Kano. Ina da shekara 24 yanzu. Na yi firamare a Unguwar Hotoro, na yi sakandire a Unguwar Tarauni duk a Jihar Kano. Daga nan sai na koma Kaduna na ci gaba da harkar waka da kuma fina-finan Hausa. Daga nan sai Allah Ya kawo ni Jihar Legas. Ga shi har yanzu muna fafatawa.
Ta yaya ka tsunduma cikin harkar waka?
Abin da ya sanya ni cikin harkar waka shi ne soyayya. A tarihin rayuwata na yi soyayya da wata yarinya da ake kira Fatima ’yar asalin Jihar Adamawa. Muna son juna. Sai na ga  na ya kamata na yi mata waka. Sai na tsara mata waka amma a lokacin sai abokaina suka rika yi mini dariya. Har Allah Ya hada ni da Adam da Misbahu Ahmad. A dakin daukar wakarsu na buga wakar, sai na yi sa’a ta karbu, sai mutane suka rika cewa ai ya kamata na ci gaba da yin waka tun da ina da fasaha da murya. Sai na ci gaba da yi har ga shi Allah Ya kawo ni Jihar Legas. Da na zo Legas sai na hadu da wani kamfani mai suna Kurmi Film Production, sai suka bukaci na yi musu waka, daga nan sai suka sanya ni a wani fim dinsu mai suna ‘Zainaba’ inda na fito a jarumi, har ta kai na yi fim uku.
Kai kake rubuta wakokinka ko kuma rubuta maka ake yi ka rera?
Gaskiya ba na ma rubuta waka da ka nake yi, ban taba rubuta waka ba tsawon shekara 11 da nake yin waka. Da na yi niyya sai kawai na ji baitoci sun rika zuwa mini. Wani lokaci ma sai ana cikin kidan sai na fara yin waka ba tare da wata matsala ba. An sha gayyata ta biki a ce na yi waka kuma nan take sai na kama yin ta.
Wadanne matsaloli ka fuskanta?
Na hadu da matsaloli masu yawa amma matsaloli biyu ne suka fi ci mini tuwo a kwarya. Na farko rashin makadi kwararre, idan mawaki ba ya shiri da makadi, to ba za ka samu abin da kake so ba, ni kuma ina da zuciya, idan na ga makadi  ba ya yi mini abin da nake so, to zan ajiye shi na je na nemi wani. Amma fa da na gane bakin zaren matsalar sai na dauki yarana na kai su suka koyi kidan suka zamo su ne makadana. A yanzu ina da yara kusan uku wadanda suke yi mini kida.
Wane buri kake so ka cimma a harkar waka?
Gaskiya burina shi ne a san ni a duniya baki daya. Na yi fice na yi suna, ko’ina a rika labarina.
Me kaka ganin yake yi wa harkar waka tarnaki a Legas?
Gaskiya har yanzu an bar mu a baya a bangaren kida. Dalili kuwa shi ne, kidan da ake yi a Kaduna da Kano da Jos ba irin sa muke yi a Legas ba. Kuma abin da ya janyo haka shi ne, bambancin iyawa da kwarewa, kuma sun fi mu dadewa a harkar.