Baiwa Daga Allah: Matatar Ɗangote ko NNPC?
Alakarsu ta nuna cewa, akwai mahaukatan shedanu a Nijeriya!
Dangantakar da ke tsakanin Matatar Dangote, wadda ita ce matatar mai mafi girma a duniya, kuma ake sa ran za ta ceto Nijeriya tare da magance matsalar man fetur da aka dade ana fama da ita a kasar wadda Kamfanin Mai na kasa (NNPC) ya kasa magance ta.
Hakazalika, yarjejeniyar da suka kulla a tsakaninsu ta haifar da damuwa da zazzafar takaddama kan rashin daidaiton manufofi da rashin bin ka’idar kudi da kuma makomar masana’antar man fetur a Nijeriya.
Alakarsu ta nuna cewa, akwai mahaukatan shedanu a Nijeriya!
Bayanan bogi
Abu na farko da ya fito fili shi ne bayanan bogi, inda tun ba a je ko’ina ba rahotanni suka nuna cewa, Kamfanin NNPCL ya saye kashi 20 cikin 100 na hannun jarin Matatar Man Dangote, alhali kuwa kashi 7.2 cikin 100 kacal na hannun jarin matatar ne NNPCL ya saya.
Amma duk da haka, wadanda suke da hannu a wannan badakala har yanzu suna kan kujerunsu, babu tambaya ko hukunci, balle sallamar su daga aiki!
Jama’a su kwana da sanin cewa, bayan almundahanar kudi, akwai batun karairayi da rashin bayar da ba’asi na gaskiya a wannan lamari.
Jami’an gwamnati da ke da hannu a irin wadannan manyan yarjejeniyoyin dole ne su bi Dokar Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB) wacce ta haramta wa jami’an gwamnati yin karya da tashe-tashen hankula da amfani da dukiyar jama’a ba bisa ka’ida ba da kuma bayar da bayanan da ba su dace ba.
A bisa dokar Kotun da’ar Ma’iakata, cin zarafi da rashin gaskiya da cin amana da dangoginsu na da hukunci mai tsanani, ciki har da sallamar ma’aikaci daga aiki!
Dambarwar ingancin mai
Abu na biyu shi ne batun ingancin mai, bayan sakamakon wani gwajin je-kana-yi-ka da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta gudanar da ya nuna cewa, man dizal din Matatar Dangote yana dauke da sinadarin sulfur da yawansa ya zarce kashi 650 a kowace miliyan (ppm).
Amma kuma, sakamakon gwajin da matatar ta gudanar a kan man dizal din da NNPC ya shigo da shi daga kasashen waje, wanda aka sayo a wasu gidajen mai guda biyu a gaban ’yan Majalisar Dokoki ta kasa da ’yan jarida, ya nuna cewa, sinadarin sulfur da man dizal din NNPC yake dauke da shi ya kai ppm 1,800 da kuma 2,000. Sakamako gwajin ya kuma nuna cewa Sulfur din da man dizal din Matatar Dangote ke dauke da shi bai fi ppm 87.6 ba.
Amma duk da haka Gwamnatin Tarayya ta bukaci a sake gudanar da gwaji.
Zargin mamaye harkar mai
Abu na uku da ake ta ce-ce-ku-ce shi ne zargin Matatar Dangote da mamaye kasuwancin mai a Nijeriya.
Matatar ta sha suka kan yadda take gudanar da harkokinta na saye da sayarwa, sannan ana zargin ta da dakile gasa tsakanin masu harkar man fetur, lamarin da ya sa gwamnati ta shiga tsakani domin tabbatar da an samu daidaito.
Sai dai kuma za a iya tuna cewa, Kamfanin NNPCL ya sanar cewa, ya sayi litar tataccen man fetur a kan N898 daga matatar, amma kuma ya hana ta bayyana ainihin farashin da ta sayar masa da man.
Uwa uba, Kamfanin NNPCL ya hana matatar sayar wa ’yan kasuwa masu zaman kansu man da ta tace? Shin wannan adalci ne ko kuma zalunci?
Kodayake a halin yanzu Kamfanin NNPCL ya amince matatar ta sayar da manta kaitsaye ga ’yan kasuwa.
Sayen danyen mai da Dala
Batu na hudu mai kama da zamba cikin aminci shi ne sayar da danyen mai a farashin Dala.
Sayar da danyen mai ga Matatar Dangote a Dala ya saba wa Kundin Tsarin Musayar Kudin kasashen Waje na Bankin CBN (2018) da Dokar Bankin CBN ta 2007, wadda ta tanadi yin amfani da Naira wajen yin kasuwanci da kamfanonin cikin guda a Nijeriya da Naira tare da tabbatar da adalci a harkokin kasuwanci.
Don haka sayar wa matatar man da Dala saba wa dokar bunkasa arzikin mai da iskar gas ta Nijeriya ce.
Amma da suka gane sun karya doka sai suka ja da baya!
Rigimar farashin mai
Abu na biyar shi ne takaddamar farashin litar man a kan N898, wadda Kamfanin NNPCL ya ce Matatar Dangote ta sayar misa.
Wannan farashin ya zarce na kayayyakin da ake shigowa da su daga waje, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Amma matatar ta karyata ikirarin na Kamfanin NNPCL da cewa, yaudara ce, tana mai jaddada aniyarta ta bin ka’idar farashin masana’antu.
’Yan zamba a ko’ina!
Abu na shida mai ban haushi shi ne yunkurin dasa ma’aikatan Kmafanin NNPCL a Matatar Dangote wadda aka gina a kan Dalar Amurka biliyan 20.
Wannan yana da babban tasiri a kan ikon cin gashin-kai na matatar da kuma sa-ido a kan aikinta.
Wannan matatar mai tana iya tace ganga 650,000 na danyen mai a kowace rana, wanda ya zarce karfin matatun mai hudu da NNPC ke da su.
Shin ma’aikatan na Kamfanin NNPCL suna da masaniyar ko kwarewa wajen sa ido kan Matatar Dangote?
Saninmu ne cewa, rashin iya aiki ne ya haifar da lalacewar matatun man guda hudu na dasa.
Alhaji Adamu Rabiu Bakondare ya rubuto daga Kaduna