Bajamushiya ta tare a jirgin kasa don kar ta biya haya
Bajamushiya ta tare a jirgin kasa don kar ta biya haya, wannan mata tana sayen tikiti ne da ke ba ta damar hawan kowane jirgi a kasar, tamkar kyauta.A lokacin da mutane ke sauka don su tafi gida su kwanta, Leonie Müller sai ta koma ciki ta lafe. Domin ita a gida take, tunda jirgin […]
Bajamushiya ta tare a jirgin kasa don kar ta biya haya, wannan mata tana sayen tikiti ne da ke ba ta damar hawan kowane jirgi a kasar, tamkar kyauta.
A lokacin da mutane ke sauka don su tafi gida su kwanta, Leonie Müller sai ta koma ciki ta lafe. Domin ita a gida take, tunda jirgin kasa ya zama gidan kwananta.
Wannan Bajamushiya, daliba ce da ke karatun digirinta a wata kwaleji, ta fice daga dakin kwantanta da take haya a lokacin bazaar. “Wannan al’amari ya faru ne, bayan da na samu matsala da mai gidan hayar da nike,” a cewar Muller, kamar yadda ta bayyana wa jaridar Washington Post a sakon i-mail. “Nan rtake na ji ba ni da sha’awar zama a gidan. A hakikanin gaskiya ma na ji ba na sha’awar zama a kowane gida,” inji ta.
“Na kan ji tamkar ina gida a jirgin kasa, kuma na samu dammar ziyartar kawaye da birane eda dama. Kai al’amarin tamkar hutu nike yi a kusan kowane lokaci,” a cewarta.
Wannan gida na matashiya ’yar sheekra 23 ya dauki hankalin kafafen yada labarai a kasar Jamus, kai har ma a shafukan sadarwar inatnet da ke baje labaran kasa, wadanda suka hada Spiegelda ta baje labarin a shafinta na intanet.
“Na kan yi karatu da rubutu, in kuma leka taga, inda nike haduwa da mutanen arziki. Kusan kodayaushe akwai abin yi a cikin jirgin kasa.” Kamar yadda Muller ta bayyana wa tashar talabijin ta SWR, a wata hira da suka yi da ita.
A halin yanzu, gogewar da ta samu ya karyata binciken da ya nuna cewa yawan tafiye-tafiye na doigomn zango na iya halaka mutum,” Sannan dangane da abin da ya shafi kasha kudi kuma, ta samu wata karuwa, inda take kasha Dala 380 a tikitin jirgi, jhar ta samu ragowar Dala 70, oin an kwatanta da kudin hayar gida da take biya na Dala 450. Sai dai ta yi nuni da cewa ba bukatarta ta samu arhar wurin zama ba.
“Ina son cusa wa mutane yin tunani akan dabi’unsu da yin nazari a kan al’amuran da suke ganin ba daidai ba ne,” a cewar Muller, lokacin da ta yi hira da the Post.
Muller na yawan tafiye-tafiye a tsakar dare, kodayake taskan yi barci a wasu gidajen ’yan uwa ko kawaye da abokai. Sai dai ta fi zama a gidan saurayinta da mahaifiyarta ko kakarta.
Wannan zama da Bajamushiya ta yi a cikin jirgin kasa ya nusar da ita wkani al’amari a harkar karatunta. Muller ta fara tattara bayanai kan irin alfanun da ta samu, kamar yadda ta bayyana a whafin sadarwarta. Kuma tana shirin rubuta wata makala a karshen karatun digirinta, da za ta yi bayani a kan yadda ta yi ta yawo a cikin jirgin kasa.