Baje-kolin burgamin Baba
Baje-kolin burgamin Baba Dubu karamin laujen silin girbi Mun karke a zubi Ci-maka mai kumbura tumbi Fafutika aikin ga ka saba Matsaloli tsibi-tsibi Datse talauci da takobi Sasari a sare da masassabi Ai maganin masu kinbibi Kyawun manufa babu munin lakabi Baba ya bude sabon babi Gandun na-duke labi-labi Mu kara doro ya na mai […]
Baje-kolin burgamin Baba
Dubu karamin laujen silin girbi
Mun karke a zubi
Ci-maka mai kumbura tumbi
Fafutika aikin ga ka saba
Matsaloli tsibi-tsibi
Datse talauci da takobi
Sasari a sare da masassabi
Ai maganin masu kinbibi
Kyawun manufa babu munin lakabi
Baba ya bude sabon babi
Gandun na-duke labi-labi
Mu kara doro ya na mai kusunbi
Mu dai tsimayi ranar girbi
kwazo na kawar wa shuka wabi
Samarin kusu sun arce
Dukiyarmu sun kwashe
Lalitarmu sun wawushe
Mai dan boto yau ta kece
Da mun yi kaura in sun zarce
’Yan matan jaba an yi bakace
Ba kama suna sai dai kwatance
Santala-kwaiduwa ta illata tsuntsaye
’Yar’didi kasuwar ajrri tai jaye-jaye
Harr tattalinmu ya balbalce
Turka-turkar tatso tunkuza
An daina hakar kuza
bula bututu har da su man kaza
Ga babban kato kazaza
Rasa kunya mai borin barhaza
An yi Asara-dan-kwabo
Dukiyrmu sun yi mata tabo
kasarmu an yi mata gyambo
Bokokon bobo
Wasu sun karke da kwambo
A farmaki fari
kamfar marka-marka na haifar da fari
karancin taki na kassara iri
Tohon tunkudowar biri
Ban da yi wa amfani cin birrbiri
Hada-hadar kasuwancin dankoli
Ana sayar da tandun kwalli
Gyara na-mujiya yai walwali
A cire wa fullo haraji da jangali
Kowwa yai aiki da hankali
Kauce wa karafkiyar koriyawa
Gabashin tsakiyar Larabawa
Burtsatsen baza bezar Birtaniyawa
Kandamar kunun Kudancin Amurkawa
Al’amuran sun harari Haurobiyawa
Girkin Girkawa
Tattalin tulun Turawa
Turuwar Turkawa
Sasarin Siriyawa
Jimurdar Jamusawa
karfanfanar kwashe asi
Kamfanin Inda-sisi
Tattalin taro da sisi
A Jihar Lallaga-sisi
Su Lasisi sun samu lasisi
’Yan makaranta
A tsanake tsaf mui bita
Da karfinmu karkaf kwata
Mu farmaki mabarnata
Da masu surutu ratatata
Baje-kolin burgamin Baba
karamin laujen silin madambaci
kasarmu za ta fice daga kunci
Mu dai mu daina tababa
A tarbi baki da tabarmar kaba
Usainin-Babajo
Zaftare harajin hajar Hajjo
A tsahirta wa cinikin gwanjo
Mun ga takun Baba-ojo
Kyakkyawan tambarin bajo
Tiren-taliya madambaci da da gashin balama dari manuniyar sama Baban-burin-huriyya ya baje kolinsu a farfajiyar Majalisar dokokin Haurrobiya, inda kannen Saurayin-kirinki da wakilan rafkiya karkashin jagorancin dogarinsu suka yi kasake don jin batutuwan da ke kunshe a kundin baje ko;lin Hauron shekara ta dubu karamin lauje da sili da tukunyar dambu. Wannan al’amari na nuni da cewa masu fuka-fukin tashi za su daina zabarin baburidon kabu-kabu, su daura damarar tukunyar dambu a wajen fardar garka da gayauna.
Kodayake an ruwaito cewa aikin haskaka Maman-Bala da birjin gada-gadar Ni-na-ja da harkar sufuri za su kwashi kaso mai tsoka, sai mu yi fatan ganin an himmatu ka’in da na’in rani da kaka don cimmma manufofin da ke kunshe cikin kundi.
Haurrobiyawa ya kamata mu tallafa wa Baba wajen aiwatar da mangartan tsare-tsare ta yadda zai ji dadin aiwatar da baje-kolin Hauron shekara mai karatowa cikin gaugawa ba tare da gigiwa ba.Takun sawun giwa ya zarta na yanyawa ba wani yawa, ballantana a yi ta kokowa.
Matukar ana so a cimmma nasara kada a yi asara, to sai Baba ya fara da haramtawa wa gwamnoninmu WAWAR WADAkAR WAUTA, musamman in ya sake jinka musu Belin-auta, da suke juya akalarsa ya zama Billen-wauta, har ta kai ganin ba a yi sa’a ba, a karke da balbalin wuta. Kuma a himmatu wajen karkata akalar dogaron da albarkatun man tunkuza, don kauce wa turka-turkar tunkuza, musamman bula bututu da takun saka rututu.
Abin da ya sa muka kira baje-kolin Hauro da burgamin Baba, domin ta haka ne kawai za a kange shi daga daga farmaki samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya, masu kwasar gararumar gyaran jar miya. Kodayake ma Iro Mugun madambaci ba zai yi musu sassauci ba.
Lallai mu yi kishi ban da kisisina da yi wa kasa kisan mummmuke, kada kowa ya noke, mu fito mu daina sake-sake, har a cimma manufar gina kasa ta hanyar aiwatar da baje-kolin Hauron shekara ta dubu karamin lauje da sili da madambaci, ko al’ummar kasarmu sun fice daga kunci. Tuni dai an yi maganin ’yan ku ci mu ci, ballantan masu shaci-fadi da suka kwaso duniya da fadi, wadanda ke haifar wa mutane radadi.