Bakano a Banki.
Wani Bakano ne mai gadin makarantar firamare, an tura masa albashi banki. Da ya je bankin don cire kudin, ya mika takardar cire kudi sai mai biyan kudin ya ce da shi: “Ba netwok.” Sai ya sami wuri ya zauna. Ya zauna na tsawon awa uku, can sai ga wani ma’aikacin bankin ya shigo ya […]
Wani Bakano ne mai gadin makarantar firamare, an tura masa albashi banki. Da ya je bankin don cire kudin, ya mika takardar cire kudi sai mai biyan kudin ya ce da shi: “Ba netwok.” Sai ya sami wuri ya zauna. Ya zauna na tsawon awa uku, can sai ga wani ma’aikacin bankin ya shigo ya zauna, jama’a na zuwa wurinsa don bukatunsu. Ai Bakanon nan sai ya mike ya nufi wani mai gadin bankin ya tambaye shi cewa: “Wancan mutumin ne network din da ake jira? Sai ya amsa da cewa bas hi ba ne. Bakano ya ce: “Na zaci shi ne netwok, da na ci masa mutunci.”
Daga Ibrahim A. B. Balarabe Zariya City, 08023442901