Bakano da kudi
Akwai wani asibiti a Jihar Borno, wanda ya kasance duk wata cutar da take damun ka, Naira dubu goma ne kudin maganin, amma idan ba ka warke ba, nan take za a biya ka Naira dubu ashirin. Da Bakano ya samu labarin haka sai ya kama yanya ya tafi Borno, wato banza ta samu. Ya […]
Akwai wani asibiti a Jihar Borno, wanda ya kasance duk wata cutar da take damun ka, Naira dubu goma ne kudin maganin, amma idan ba ka warke ba, nan take za a biya ka Naira dubu ashirin. Da Bakano ya samu labarin haka sai ya kama yanya ya tafi Borno, wato banza ta samu. Ya je asibitin ya ce wa likita: “Ba ni da lafiya.” Likita ya ce masa: “Me ke damun ka?” Ya ce: “Ba na jin dandano ne a harshena.” Bakanon kuma lafiyarsa kalau, kawai shi dai bukatarsa ya samu Naira dubu goma, domin zai ce wa likita bai warke ba. Likita ya ce masa: “Naira dubu goma ne kudin maganin, amma idan har ba ka warke ba, za mu ba ka Naira dubu ashirin.” Cikin gaugawa ya biya kudin, sai likita ya ce: “Nas, ki bude akwati na 27, ki dauko wannan maganin ki ba shi cokali daya daya tak.” Ta dauko magani ta zuba cokali daya ta ba Bakano. Yana shan maganin sai ya amayar da shi. Ya ce wa likita: “Likita! Ai wannan ba magani ba ne.” Likita ya ce: “To idan ba magani ba ne, mene ne?” Ya ce: “Ai wannan fitsari ne!” Sai likita ya ce: “Yauwa, ka ga Allah Ya ba ka lafiya, dandanon harshenka ya dawo daidai, tashi ka tafi, Allah Ya kara maka lafiya.”
Daga Malam Babaji Na Khalisa Hadeja, 07068068315