Bakano dan shekara 23 malamin koyar da tukin jirgin sama a Amurka

Mubarak Bashir dan shekara 23 shi ne baki na farko da makarantar koyar da tukin jirgin sama da ke Amurka ta taba dauka a matsayi mai bayar da horon tukin jirgi a tarihin makarantar. Mubarak dan asalin garin Sitti da ke karamar Hukumar Sumaila ta Kano ya zanta da wakilinmu akan irin kalubalen da ya […]

Bakano dan shekara 23 malamin koyar da tukin jirgin sama a Amurka
Bakano dan shekara 23 malamin koyar da tukin jirgin sama a Amurka

Mubarak Bashir dan shekara 23 shi ne baki na farko da makarantar koyar da tukin jirgin sama da ke Amurka ta taba dauka a matsayi mai bayar da horon tukin jirgi a tarihin makarantar. Mubarak dan asalin garin Sitti da ke karamar Hukumar Sumaila ta Kano ya zanta da wakilinmu akan irin kalubalen da ya fuskanta a matsayinsa na baki a cikin Turawa.

Ka ba mu takaitaccen tarihinka?
Suna na Mubarak  Bashir, an haife ni a shekarar 1992. Shekaruna na haihuwa 23, ni dan asalin garin sitti da ke karamar Hukumar Sumaila a Kano. Na yi karatun firamare a kwalejin SeaGate da ke Legas, daga nan na shiga Zaria Academy, don karatun gaba da firamare. Na kuma halarci Jami’ar Luton East London Unibersity da ke Malesiya inda na yi digiri na farko a fannin masarrafar kwamfuta (software). A yanzu haka ni malami ne a makarantar koyon tukin jirgin sama, wato Aerosim flight Academy da ke Florida a kasar Amurka.
Ya ya ka samu shiga wannan makarantar, kuma wa ya dauki nauyin ka?
Bayan na gama karatun digirina na farko, sai na ji ina sha’awar koyon tukin jirgin sama. Saboda haka na shaida wa mahaifina, wanda bai taba yin kasa a gwiwa ba, wajen ganin mun samu ingattaccen ilimi a matsayinmu na ‘ya’yansa.
Da na shaida masa bukata ta, sai ya ce da ni ba komai za a yi. Na nemi gurbin karatu a wannan makarantar na kuma samu. Karatuna na yi shi ne karkashin daukar nauyin da mahaifina ya yi na wannan karatun. A gaskiya mahaifinmu ya kan so ya ga mun samu duk wani abu na inganta rayuwarmu, saboda haka ya taka rawa sosai wajen ganin na cimma burina a rayuwata.
Ya za ka kwatanta karatu a kasar Amurka da gida Najeriya?
A gaskiya yanayin karatu a wadannan kasashe abubuwa ne mabambanta ta fuskar da mai yinsu ya kale su. In ana maganar kwatanta kasashe biyu masu bambancin al’adu da addini da tattalin arziki, to kuwa tabbas yanayin karatu a wadannan kasashen ba zai zamanto iri daya ba.
Idan ana maganar karatun tukin jirgin sama ne, to zan iya cewa yanayin garin Florida ya yi daidai da na koyon tukin jirgin sama. Hakazalika in ana batun kayan aikin koyon tukin jirgin sama kuwa tabbas Amurka ta fi Najeriya.
Me ne dalilin da ya sa mutanen Najeriya suka fifita karatu a kasashen waje fiye da gida?
Tabbas mutanen kasarnan na fita zuwa kasashe da dama don neman ilmi, haka zalika wani abu guda da ba za a iya dauke shi daga cikin hujjojin fitar ba shi ne; kowa na bukatar ilmi mai inganci.
Wadanne kalubale ka fuskanta a can?
Ina ganin babban kalubalen da na fuskanta shi ne karancin shekaruna. Na tsinci kaina a wani yanayi na kowa ya grime ni. Ga ni da karanci shekaru a kuma garin da ba uwa ba uba, saboda haka ya zame min tilas yin taka tsan-tsan a dukkanin al’amurana.
Haka zalika a bangaren karatuna, ba abu ne mai sauki ba ga mai karancin shekaru iri na a wannan fannin ba. Kasancewa kwararren matukin jirgin sama na bukatar jajircewa da aiki tukuru, wadannan su ne sirrin koyon aikin gami da addu’a. Wadannan abubuwa sun taimaka min kwarai.
Ko ka fuskanci tsangwama kasancewarka bakar fata a wannan makarantar?
A gaskiya ba zan iya tuna wani lokaci da aka ci zarafina wai don ni baki ba ne. Haka zalika kasancewata bakin mutum na farko da wannan makaranta ta taba dauka a matsayin malami ya kara tabbar da cewar ana daukar kowa daidai babu bambancin launin fata.
Mene ne sirrin samun kwarin gwiwarka ?
Na farko dai sha’awar da nake da ita wajen ganin na koyi tukin jirgin sama, na biyu kuma shi ne sha’awata ga yawo cikin jirgin sama da kuma son haduwa da mutane daga sassa daban na wannan duniyar, wadanda kuma muke da bambancin al’adu da sauran abubuwa.
Sannan goyon baya da gudnmuwar da mahaifina ke ba ni sun taka muhimmiyar rawa har na kai ga wannan mataki a yau. Tabbas mahaifina bai gaza ba wajen ganin burina ya cika.
Kwanannan kasar Amurka ta ba ka aiki a matsayin mai koyar da tukin jirgin sama a kasar. Me za ka iya cewa game da hakan?
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Mai kowa, Mai komai. Mafi akasarin wadanda kan zo nan koyon tukin, sukan koma gida da zarar sun samu lasisin tukin jirkin sama na kasuwanci. To amma ni na zabi in tsaya don in kara samun horo, in kuma samu lasisin koyar da tukin jirgin saman.
Ina ganin daurewar da na yi na tsaya na kara samun horo da wancan lasisin sun taimaka, wajen samun Biza ta fI wacce da ita ne za ka iya samun aiki a gwamnatance a kasar Amurka.
Kana da shirin dawowa gida Najeriya kuwa?
Ba ni da wata kasa wacce ta wuce Najeriya, tabbas zan dawo gida Najeriya domin ita ce kasata.
Mene ne burinka nan gaba?
Yanzu dai tun da na samu nasarar samun wannan aikin na koyarwa, zan dukufa wajen ganin cewa na aiwatar da wannan aikin daidai gwargwado. Bayan wannan watakila in tuka jirgi kafin in bude tawa harkar.