Bakano ya sanya wa babur mai kafa uku talabijin da wurin cajin waya
Wani saurayi, Umar Marmara, ya kawata babur din da yake sana’arsa ta haya da shi da talabajin da kuma wurin cajin waya a Kano.
Wani saurayi, Muhammad Al Amin, ya kawata babur din da yake sana’arsa ta haya da talabajin da kuma wurin cajin waya a Kano.
Muhammad ya yiwa babur dinsa mai kafa uku kwaskwarima, inda ya makala talabijin na bango kirar Plasma a ciki, ta yadda idan ana tafiya fasinja za su rika yin kallo domin debe kewa.
- Obasanjo ya yi direban Keke Napep na yini daya
- An kafa dokar hana acaba da haya da Keke Napep a Kogi
A hirarsa da Aminiya, Al Amin ya kara da cewa, “Na sa kayan cajin waya daban-daban har guda goma sha daya, yadda zai kasance duk irin wayar da ka zo da ita za ka iya sa caji, kuma ko ku nawa ne.”
A cewarsa, sakamakon kwaskwarimar da ya yiwa babur din nasa, ya samu alheri mai yawa daga mutanen da ke zuwa su hau daga ciki da kuma wajen Kano.
Sannan bai kara ko kwabo ba a farashin da ake daukar mutane zuwa ko’ina ba a cikin garin Kano.
Ya bayyana cewa da farko ya sa talabijin din ne domin amfanin kansa, saboda a duk lokacin da aka dauke shi shata, idan suka je wani wuri aka ajiye shi yana jira, sai ya kunna ya rika yin kallo.
Amma daga baya sai hakan ya burge jama’a, har suna sha’awar hawa babur din nasa, suna tafiya, suna kallon talbijin har su je inda za su sauka.