Bakano ya shiga hannu kan yunkurin garkuwa da wani a Edo

An gano wanda ake kokarin yin garkuwa da shi ya taba taimakon matashin a baya.

Bakano ya shiga hannu kan yunkurin garkuwa da wani a Edo

‘Yan Sanda

Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta cafke wani matashi dan asalin Jihar Kano da ya yi barazanar yin garkuwa da Shugaban yankin Hausawa a Edo, Alhaji Badamasi Saleh.

An rawaito cewar an cafke matashin ne bayan korafi da Alhaji Badamasi Saleh ya shigar ofishin ’yan sanda na birnin Benin.

Saleh ya shigar da karar ne a ranar 16 ga watan Satumba, inda ya bayyana cewa matashin na masa barazanar cewar zai yi garkuwa da shi.

Sai dai wanda ake zargin ya shaida wa Saleh cewar wani makusancinsa ya biya shi kudi miliyan daya don ya yi garkuwa da shi, amma ya kasa saboda kasancewarsa mutumin kirki.

Sai dai wanda ake zargin ya tilasta wa Saleh ya biya shi miliyan daya don fasa yin garkuwar da shi.

Amma daga bisani jami’an tsaro sun bukaci wanda ake zargin da ci gaba da yin basaja ga wanda yake son ba shi kudi don yin garkuwa da shugaban Hausawan yankin.

Kakakin ’yan sandan Jihar, Kontongs Bello, ya tabbatar da cafke matashin, inda ya ce an kama shi lokacin da ya ke karbar wasu kudade.

Ya ce wanda ya shigar da kara, ya amince da biyan N100,000 a asusun ajiyar bankin wanda ake zargin.

Kakakin ya kuma ce an cafke shi a wata maboya lokacin da ake kokarin tabbatar masa da saka kudin cikin asusun bankin da ya bayar.

Kontongs, ya ce bayan gudanar da bincike, an gano cewar mutumin da ya shigar da karar ya taba taimakon matashin a baya.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya