Bakanuwa ta zama mace ta farko mai horas da ’yan wasan kwallon kafa

Na shiga harkar tamaula bayan rasuwar mijina.

Bakanuwa ta zama mace ta farko mai horas da ’yan wasan kwallon kafa

Fatima Dahiru, ’yar asalin jihar Kano, ta zamo mace tilo a Najeriya da ke horas da ’yan wasan kwallon kafa, bayan zamowa kocin kungiyar kwallon kafa ta Manya United.

A tattaunawarta da kafar yada labarai ta TRT, Fatima mai shekaru 39 a duniya ta ce tun tana karama take kaunar kwallon kafa.

Sai dai ta ce gudun maganganun mutane ya sa ba ta taba bugawa ba har sai da mijinta ya rasu da ta fara horas da ’yan wasan.

Fatima ta kuma ce duk da tana shan suka daga mutane, hakan ya daina damunta kamar a baya, tunda ta fahimci muhimmacin kallon kafa ga rayuwarta.

“Lokacin da mijina ya rasu, na shiga tashin hanakali sosai har na daina shiga mutane. Lokacin da kawai nake farin ciki shi ne idan na jiyo yaran unguwarmu na wasan kwallo a layinmu.

“A yanzu dai burina shi ne kafa kungiyar kwallon kafa ta mata zalla da izinin Allah,” in ji ta.

Kungiyar Manya United dai ta samu nasarar cin kofi har uku a wasannin da Fatima ta jagoranci horas da ’yan wasan kungiyar.