Bakin cikin mata da da sun sa magidanci ya banka wa kansa wuta a Katsina
Wani mutum mai suna Sani Salisu dan asalin karamar Hukumar Musawa da ke aiki a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina ya banka wa kansa wuta cikin dare a ranar Asabar da ta gabata a garin dandagoro da ke karamar Hukumar batagarawa. Babu wanda ya san ko daga ina Sani ya shiga harabar da ke kusa […]

Wani mutum mai suna Sani Salisu dan asalin karamar Hukumar Musawa da ke aiki a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina ya banka wa kansa wuta cikin dare a ranar Asabar da ta gabata a garin dandagoro da ke karamar Hukumar batagarawa.
Babu wanda ya san ko daga ina Sani ya shiga harabar da ke kusa da babbar kofar nan da ke maraba da zuwa Katsina (Welcome to Katsina) a cikin duhun dare inda ya je karkashin wata itaciyar bedi ya zuba wa kansa fetur ya kunna wuta.
Wadanda suka shaida faruwar abin sun fada wa Aminiya cewa, yara ne suka fara ganinsa bayan sun je yin bahaya inda daga bisani aka nemi daukin jama’a don ceto rayuwarsa.
“Da farko an yi zaton almajiri ne wutar ta kama,” kamar yadda wani daga cikin masu kai daukin mai suna Kabir Sa’idu dandagoro ya shaida wa Aminiya,”A lokacin da jama’a ta yunkuro ana kokarin kashe wutar mun ji yana cewa, “ni na kunna wa kaina wuta saboda bakin cikin matata da dana da suka guje ni duk da ina fama da rashin kafa daya,” inji dandagoro.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Faruwar hakan bai ba su mamaki ba domin ’yan lokutan da yake shigowa cikin garin wajen abokan arziki da masu ba shi taimako domin wani lokaci yana neman taimako tamkar almajiri duk da cewa babban ma’aikaci ne, yakan ce mutuwarsa ta fiye masa da irin halin da yake ciki.”
Majiyar ta ce, bai dade da yin irin wannan furuci aka zaunar da shi aka yi masa nasiha da wa’azi a kan irin kalaman da ake yi ba, an yi iya kokarin jin halin da yake ciki amma ya ki ya bayyana. Kamar yadda Aminiya ta kalato har akwai lokacin da wani abokinsa ya dauke shi don mayar da shi garinsu Musawa amma a hanya ya sulbe.
Da Aminiya ta tuntubi Magajin dandagoro Alhaji Muttaka Magaji ya tabbatar da faruwar hakan inda ya ce, “Ba mu san mutumin ba domin ba a nan yake zaune ba, sai dai kawai kamar yadda labari ya zo mana, an ce dan asalin Musawa ne da aiki ya kawo shi Katsina. Akwai hasashen cewa ya zo wurin ne a motar haya kasancewarsa mai kafa daya da yake amfani da sanduna.”
Ya ce muumin mai suna Sani Salisu ma’aikaci a ma’aikatar lafiya ta Jihar Katsina da ya kwashe kimanin shekara 30 yana aiki. “Har ya zuwa yanzu babu wani labari da ya zo gare mu na ita matar da yake fadi wadda bai ambaci sunanta ba, ko wani daga cikin dangi ko wasu da suka san shi ba, ko kuma wane irin bakin ciki ne iyalinsa nasa suka sanya shi da har ya aiwatar da wannan danyen aiki da dare a inda babu kowa,” inji Magajin.
Wani malamin asibiti a babban asibitin Katsina inda aka kai Sani, Malam Aminu Suleiman ya ce, Sani ya samu mummunar kuna da zai yi wuya ya rayu.
Kuma kafin wakilinmu ya kammala hada wannan rahoto ya samu tabbacin cewa Allah Ya amshi ran Sani Salisu.
Wannan ne karo na biyu da aka samu ma’aikatan wannan ma’aikata da kashe kansu, idan za a tuna a wani lokaci baya an samu wani ma’aikacin hukumar lafiyar da ya kashe kansa ta hanyar ratayewa a cikin wani daji da ke hanyar zuwa Kaita daga garin Shinkafi.