Bakin haure 50,000 sun mutu a hanyar neman ingantacciyar rayuwa —IOM
Hukumar ta ce babu wani kokarin kirki da kasashe ke yi don shawo kan matsalar bakin haure balle hana aukuwar hakan.
Hukumar Kula da Masu Hijira ta Duniya (IOM) ta ce akalla bakin haure 50,000 ne suka mutu a fadin duniya.
Hukumar ta ce bakin hauren sun mutu ne bayan jefa rayuwarsu cikin hadarin yin kaura zuwa kasashen waje don samun ingantacciyar rayuwa.
- NAJERIYA A YAU: Rikicin PDP: Shin Atiku zai kai bantensa a 2023?
- A Najeriya aka buga sabbin takardun kudi —Buhari
“Yayin da akan samu dubban bakin hauren da ke mutuwa a hanya duk shekara, babu wani kokarin kirki da aka yi don shawo kan matsalar balle hana aukuwarta,”inji hukumar.
IOM ta bayyana a cikin wani sabon rahotonta da ta fitar ranar Laraba, cewa wannan adadi na wadanda suka mutu ne tun daga 2014.
Rahoton hukumar ya nuna babu wani kokarin a-zo-a-gani da kasashe ke yi don kula da lamarin bakin haure a yankunansu.