Bakin kishi: Maigida ya kashe matarsa da dansa

Sai da ya sha tabar wiwinsa ta yi masa karo sannan ya hallaka iyalansa.

Bakin kishi: Maigida ya kashe matarsa da dansa

Wani magidanci da ake zargi da kashe matarsa saboda bakin kishi ya ce ya aikata hakan ne bayan ya sha tabar wiwi ta yi mishi karo.

Mutum wanda ya ce ya yi amfani shebur ne ya kashe matar tasa da dansa saboda sabanin da suka samu a lokacin da yake cikin maye, bai san abin da ya aikata ba sai da hankalinsa ya dawo mishi a ofishin ’yan sanda.

“Na koma gida da rana ne domin in ba wa matata karin kudin cefane saboda ban bar mata isasshen kudi ba, amma sai na iske ta da wasu bakin mutane, wanda hakan ya kona min rai sosai saboda na yarda da ita.

“Ta yi ta kokarin yi min bayani amma na ce atafau, na wuce na je na sha tabar wiwina ko zai kwantar min da hankali.

“Amma da na sha ta yi min karo sai na kasa danne zuciyata,” inji shi, a lokacin da ake gabatar da shi ga manema labarai kan lafin da ake zargi ya aikata a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Anambra.

Ya yi zargin cewa shaidanin da ke tare da shi ne ya yi sanadin hallaka matar da dan nasa.

“Ban dawo cikin hayyacina ba sai da na bude ido na gan ni a ofishin ’yan sanda.

“Na yi mamakin cewa ni da kaina ne na aikata hakan ga matar da nake so sosai; domin ita ce kadai abin da ya rage min,” inji shi

Ya ce shekaransu biyar da aure bayan sun shekara shida suna soyayya da matar tasa da ya kashe.

“Na san na aikata babban laifi, amma ba a cikin hankalina na aikata ba,” inji mutumin wanda ya ce shi tsohon mai wa’azin Kirista ne, amma da al’amuran rayuwa suka dagule masa, sai ya koma shaye-shaye.

“Mu guji shaye-shaye musamman tabar wiwi domin ba kyau… idan ka sha ta sai shaidanin da ke jikinka ya fi karfinka,” inji wanda ake zargin.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya