Bakin Kwari Masu Wari Sun Bulla a Ondo
Wasu bakin kwari masu wari sun mamaye gidaje da gonaki, wanda hakan ya sa jama’ar kaura daga gidadensu da gonakinsu a kauyen Afin Akoko da ke Karamar Hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma a Jihar Ondo. Wakilinmu ya ruwaito cewa da yawa daga cikin mazauna yankin wadanda akasarinsu manoma ne yanzu haka suna gudun hijira […]
Wasu bakin kwari masu wari sun mamaye gidaje da gonaki, wanda hakan ya sa jama’ar kaura daga gidadensu da gonakinsu a kauyen Afin Akoko da ke Karamar Hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma a Jihar Ondo.
Wakilinmu ya ruwaito cewa da yawa daga cikin mazauna yankin wadanda akasarinsu manoma ne yanzu haka suna gudun hijira sakamakon bala’in.
Wani mazaunin garin kuma manomi mai suna Abu Balogun, ya shaida wa Aminiya cewa warin da kwari ke yi zai iya haifar da annoba matukar gwamnati ba ta yi gaggawar magance matsalar ba.
- Dan China Ya Kashe Budurwarsa A Abia
- Manufofin Gwamnatin Tinubu ne silar taɓarɓarewar rayuwa a Najeriya —ACF
“Mun yi kokarin kashe kwarin ta hanyar amfani da ruwan zafi da Gammalin 20 amma ba sa mutuwa, ina kira ga jama’armu da su yi taka-tsan-tsan a yanzu.
“Yayin da nake magana da ku, mutane ba sa iya dafa abinci ko cin abinci a tsakar gida saboda tsoron kamuwa da cuta. Muna shan bakar wahala, muna nemanr taimako.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, sarkin garin, Farfesa Abduraheem Mustapha Adejoro, ya ce “halin da ake ciki a garin yanzu yana da muni”
Oba Adejoro ya bayyana cewa an tattauna lamarin a majalisar Oba ranar Litinin. Ya yi yi kira ga hukumomin lafiya na gwamnati da su zo Afin Akoko su dauki matakan da suka dace.
Kwamishinan lafiya na jihar Ondo Banji Ajaka, ya ce gwamnati ta himmatu wurin maganin kwarin kuma tuni ma’aikatarsa ta hada kai da ma’aikatar muhalli domin kauce wa barkewar cututtuka da kwari ke iya samarwa.