Bakin makiyaya ne ke haddasa rikici a Najeriya – Gwamnan Oyo

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya ce wajibi ne a hanzarta daukar tsauraran matakai a kan bakin makiyaya da suke shigowa cikin kasa daga wasu kasashe suna haddasa fitina. Ya ce makiyayan cikin gida ba su da matsala domin gwamnati ta gano cewa bakin makiyaya ne suka haddasa rikici a Jihar Benue da wasu […]

Bakin makiyaya ne ke haddasa rikici a Najeriya – Gwamnan Oyo

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya ce wajibi ne a hanzarta daukar tsauraran matakai a kan bakin makiyaya da suke shigowa cikin kasa daga wasu kasashe suna haddasa fitina. Ya ce makiyayan cikin gida ba su da matsala domin gwamnati ta gano cewa bakin makiyaya ne suka haddasa rikici a Jihar Benue da wasu jihohi.

Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Talata da ta gabata ta hanyar jawabinsa wanda da mai ba shi shawara a kan tsaro, Mista Segun Abolarinwa ya karanta a madadinsa a wajen taron masu ruwa da tsaki da rundunar ’yan sanda ta shirya domin tattaunawa a kan yadda za a yi maganin rikicin makiyaya da manoma a Jihar Oyo.

Ya ce matakin da gwamnati ta dauka a baya shi ne ya sa aka samu saukin matsalar rikicin manoma da makiyaya a jihar. Ya ce, “za mu ci gaba da daukar irin wannan mataki domin tabbatar da an yi maganin rikicin manoma da makiyaya wadanda shekaru da yawa da suka wuce suke tare da da mu’amala da kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu.”    

Shi kuwa Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo cewa ya yi, irin yadda ake samun barkewar rikicin manoma da makiyaya a wasu sassan kasar nan, shi ne ya sa ya kira wannan taro domin kowa ya tofa albarkacin bakinsa a kan yadda za a yi maganin wannan matsala a jihar. Ya tunatar da taron a game da matsayin ’yan sanda na tabbatar da doka da oda da kare lafiya da dukiyar jama’a domin samar da zama lafiya da kwanciyar hankali.

Wasu daga cikin manoma da suka halarci taron sun ce ci gaba da shiga cikin gonakinsu da dabbobin makiyaya ke yi da cinye amfanin gano da lalata su shi ne yake kara ruruta wutar fitina a tsakaninsu da makiyayan. Su kuwa makiyayan sun nuna cewa ya kamata a samar da burtali na dindindin da za su rika kiwon dabbobinsu a ciki kuma a ja kunnen manoma su daina zuba gubar magani a cikin ruwa da dabbobinsu suke ci suna mutuwa.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Jihar Oyo, Alhaji Yakubu Bello ya shaida wa Aminiya cewa: “A gaskiya gwamnatin jihar tana yin sako-sako da wannan al’amari domin ba ta yin aiki da abin da ta fadi. Idan har za ta yi aiki da abin da take fadi to kuwa za a samu sauki amma abin bakin ciki shi ne, a wajen irin wannan taro ake fadin irin matakan da za a dauka amma a nan ake barin maganar ba tare da aiwatarwa ba.”

Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin da Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad dahiru Zungeru da Sarkin Nufawan Ibadan Alhaji Shehu Ibrahim suna daga cikin mahalarta taron.