Bakinta ya ki rufuwa bayan ta kyalkyata dariya
Likita ya yi kokarin rufe bakin wata ’yar kasar China bayan ta yi dariya, inda muka-mukinta ya ki komawa daidai. Wannan abu ya faru ne a ranar 1 ga Satumban nan lokacin da matar take cikin wani jirgin kasa a hanyarta ta zuwa tashar jirgin da ke Kudancin Guangzhou. Dokta Luo Wensheng, na cikin fasinjojin […]
Likita ya yi kokarin rufe bakin wata ’yar kasar China bayan ta yi dariya, inda muka-mukinta ya ki komawa daidai.
Wannan abu ya faru ne a ranar 1 ga Satumban nan lokacin da matar take cikin wani jirgin kasa a hanyarta ta zuwa tashar jirgin da ke Kudancin Guangzhou. Dokta Luo Wensheng, na cikin fasinjojin jirgin wanda ya taso daga garin Kunming babban birnin Yunnan da ke Kudu maso Yamma, kuma an yi wa matar aikin a asibitin Liwan wata cibiya ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Guangzhou bayan likitan ya samu sanarwar gaggawa ta kafar labarai don bayar da agajin gaggawa ga fasinjar.
Da jin sanarwar neman agajin sai likitan ya yi gaggawa zuwa don taimaka wa fasinjar da bakinta ke bude ya ki rufuwa, inda hakan ke nuna cewa tana fuskanta matsalar shanyewar wani bangaren muka-mukinta. Sai dai an gano ba ta da cutar hawan jini. Wani da yake magana da matar ce ya fahimci cewa, bakinta ya ki komawa yadda yake bayan ta yi dariya mai karfi.
“Matar ta yi ta zubar da yawu dalalal bayan bakinta ya ki rufuwa, kuma da farko na yi tunanin tana dauke da cutar shanyewar barayin jiki ne,” Luo Wensheng, ya bayyana wa kafar labarai ta Guancha News. “Ganin halin da take ciki sai na yi mata gwajin hawan jini tare da yi mata wasu tambayoyi, sannan na fahimci cewa, lallai ta gaza amfani da muka-mukinta,” inji shi.
Duk da yake Luo, ba kwararre ba ne a fannin kiwon lafiya, sai ya kasance abin ya yi masa wani iri ta yadda ya rasa hanyar da zai bi don saita fuskar matar. Sai ya fada mata cewa zai taimaka mata amma abu ne mai hadarin gaske a saita muka-mukin. Amma duk da haka matar ta bukaci ya gwada koda zai iya.
Luo, ya kara da cewa, “Wannan matar duk jijiyoyin jikinta sun yi rauni kamar ba ta da lafiya. Kamar yadda likitan farko da ya duba ta ya sanar. Na bai wa matar shawara a kan ta tafi asibiti, amma sai ma’aikatan asibitin suka ce akwai sauran awa daya kafin su isa inda za su tsaya. Sai na fahimci cewa, matar na cikin damuwa a wannan lokaci, ganin haka sai na ci gaba da kokarin saita muka-mukinta ta yadda bakin zai rufu.”
A wannan lokacin da Dokta Luo, ya yi kokarin saita muka-mukinta a karshe matar ta ji zafi matuka, amma kuma ya yi nasara. Hakan ya sa ta rufe bakin. Matar ta yi wa Luo godiya mai yawa, ta ce, muka-mukinta ya fara gocewa ne lokacin da take dauke da juna biyu saboda tana yawan amai. A cewarta idan muka-mukin mutum ya taba gocewa, akwai yiwuwar ya sake yin haka, musamman lokacin da yake yin hamma ko dariya kuma ya bude bakinsa sosai.