Bako da dan kasa!
Yau amsa wata tambaya da ake ta yi mini a ’yan kwanakin nan zan yi, musamman bayan na saki rahoton kwayar halittar da aka binciko game da asalina da inda iyaye da kakanni da kakannin, kakannina suka taso, har muka zama zama ’yan kasa da a yau ake ce da mu Hausawa. Ni abin da […]
Yau amsa wata tambaya da ake ta yi mini a ’yan kwanakin nan zan yi, musamman bayan na saki rahoton kwayar halittar da aka binciko game da asalina da inda iyaye da kakanni da kakannin, kakannina suka taso, har muka zama zama ’yan kasa da a yau ake ce da mu Hausawa. Ni abin da binciken da kimiyya ya tabbattar min yanzu ba abin mamaki ba ne, wato wai da ake cewa a duniyar yau ba wadansu da za su gaje wani yanki su ce nasu ne, wadanda suka iske su a wurin kuma, su ne baki. A doron kasa a yau, ba wani bako ko dan kasa, kowa bako ne!
Idan muka natsu muka yi nazari za mu fahici cewa kusan dukkan wata al’umma da ta samu kanta a wani yanki ko wurin zama, ba za ta iya cewa nan ne mazauninta na farko ba ko kuma na karshe. Saboda haka idan Hausawa ba inda suke a yau shi ne mazauninsu na farko ba, ba kuma za mu iya cewa shi ne na karshe ba, haka kuma duk wata al’umma da ke doron kasa. Turawan Turai ba halittattun wurin ba ne. Larabawa yawancinsu Asiyawa ne. Su kuwa Turawan Amurka, ai gyauron Indiyawa ne da Turawan Turai, tunda dadewa.
Haka abin yake a Astireliya, domin kuwa duk masu mulkinsu da sauran miliyoyin jama’ar kasar da yanzu suke ganin su ne ’yan kasa, ba za su kore Aborijin din kasar ba da ake jin cewa su ne asalin kasar. Wannan yanayi haka yake a cikin Nahiyar Afirka, ta yadda ba wata kasa da za ta ce ita ce ’yar kasa ga kuma baki a cikin nahiyar. Haka ko cikin kasashen da ake da su a Nahiyar Afirka, ba wata al’umma da za ta ce ita ce uwa, ga kuma wasu da za ta kira a matsayin ’ya’ya ko bayi ko baki.
Shin ina bakaken fatar Amurka da Faransa da Ingila da Holand da wasu kasashe da dama, su kuma ’yan kasan ne ko baki a cikin wadannan kasashe?
Saboda haka idan aka ce za a ci gaba da rarrabuwa irin ta dan kasa da bako, irin yadda muke faman yi yanzu a Najeriya da wasu sassan duniya, to kuwa mun shiga uku, mun lalace, domin kuwa ba mai iya cewa ga asalinsa, ga kuma wanda ya kasance bako a cikin kasarsa ko al’ummar da yake zaune a ciki. Bayarben Oyo da na Ife da kuma Ogbomosho duk zuwa suka yi wadannan wurare, idan har wasu sun same su a cikin yankinsu daga baya, suka yi shekaru aru-aru tare, bai kamata a ce su kuma sun kasance baki ba, domin kuwa ai bako ba ya korar bako. Haka wannan yanayi yake ko a tsakanin Ibo da Hausawa da sauransu. Duk wanda ka gani yana zaune a wuri, to tabbata kaka da kakanninsa zuwa suka yi, ba wani da zai ce don ya sari wuri ya zauna, shi ne ya samar da wurin, kuma koda wani ya zo daga baya ya sari wuri ya zauna shi ma, shi ke nan shi kuma ya zama bako! Shin da Bagauda ya soma sarar birnin Kano shekaru aru-aru da suka wuce, yana nufin cewa wadanda suka rayu a cikin tsohon birnin na Kano ko Santolo da wadanda suka yi hijira zuwa sabon birnin, akwai bako da dan gari? Shin su Barbushe da ’ya’yansu da jikoki da ma tattaba kunne da suka rayu zuwa yau su ne ’yan kasa ko kuwa baki, ko kuwa za mu ce ai ’ya’ya da jikokin Bagauda su ne ’yan kasa ko kuma su ma bakin ne a Kano?
Wannan shi ya kamata mu yi tunani a kai. Mu tamu matsalar a halin yanzu ba ta wuce wa ya riga wani zama a wuri ba. Idan aka dubi lamarin da kyau za a ga cewa ba ma inda matsalar ta fi kamari irin yadda a halin da ake ciki wadansu ke kallon wadansu a matsayin ba ’yan kasar da aka sansu a ciki ba, ba kuma tare da wata hujja mai karfi ba. Ta yaya in ba neman ta da zaune-tsaye ba, mutumin da ke cikin jihohin Filato da Binuwai da Taraba da wasu sassan na jihohin Neja da Kogi da sauran jihohi makusanta, zai ce shi ba dan Arewa ba ne, wai shi dan Midil Bel ne? Wace ce kuma Midil Bel, a wace kasar take, yaushe ta samo asali? An yi wadannan tambayoyi domin kuwa tunani ba ya iya daukar wannan kwamacala. Idan yau aka ce za a raba kasar nan a fitar da Midil Bel, daga ina za a tsaga, kuma a ina za a tsaya? Mu tuna fa rarrabuwa a tsakaniumu ba abin da za ta kawo sai rashin zama lafiya da dimuwa da kuma bakin kishi da zai kai mu ga kashe-kashen juna da ta da kayar bayan da ba gaira ba dalili.
Saboda haka lokaci ya yi da za mu fahimci irin mugun halin da muke neman mu sanya kanmu a ciki a halin yanzu. Ba wani dan kasa ko bako a cikinmu, idan kuma akwai wani da ke ganin cewa shi ne dan kasa saura kuma baki ne. To ya koma ya tambayi mai dattin hula idan yana da rai ko kuma ya tambayi na kusa da shi game da asalinsa na gaskiya, ina tabbatar masa cewa zai gane cewa ko dai daga gabas ya fito ko kuma daga kudu ko yamma ko kuma arewa, don kuwa ba wanda ya bubbugo daga karkashin kasa ko ya fado daga sama.
Saboda haka ko ana so ko ba a so, Ibo dan uwan Balarabe ne shakiki, haka kuma Bafullatani da Balarabe, kamar yadda Bahaushe yake da mutanen Asiya ko Indiya. Haka wannan dangantaka take tsakanin Turawa da Amurkawa, ko kuma Amurkawa da Indiyawa. In haka ne, kuma hakan ne to mene ne na ta da hankali tsakanimu a nan cikin Najeriya da kuma makwabta? Lokaci ya yi da za mu gane gaskiya domin mu bi ta, mu kuma fahimci karya da masu shirya ta, domin mu kauce mata! Ba kuma wata hanya ta yin hakan sai mun yi watsi da tunanin dan kasa da bako a zukatanmu, mu dauki kowa a matsayin dan uwa da fatar kunnuwanmu suna ji, domin jiki ya tsira!