Bako da hura

Wata rana wani mutum ya je gidan surukasa, ya tarar ana kirbin hura. Da aka gama sai aka aka kawo, aka ajiya a dakin da yake. To akwai wani yaro a kwance a dakin. Da kwadan hurar ya kama shi, kafin a dama ma shi sai ya sa hannunsa ya gutsura. Sai yaron nan ya […]

Bako da hura
Bako da hura

Wata rana wani mutum ya je gidan surukasa, ya tarar ana kirbin hura. Da aka gama sai aka aka kawo, aka ajiya a dakin da yake. To akwai wani yaro a kwance a dakin. Da kwadan hurar ya kama shi, kafin a dama ma shi sai ya sa hannunsa ya gutsura. Sai yaron nan ya ce: “Iya ya gutsuri hura.” Jin haka sai ya yi sauri ya maida. Sai yaron ya kara cewa: “Ya maida.” Sai ya yi wa yaron dakuwa, sai ya ce: “Iya ya zage ni!”
 Daga Rufa’i H. Funtuwa, 08159005778