Bakon dundumin Dubarudu

A rana ta sili da manuniyar kasa ga watan Ukun-tutun-baba, na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, na hadu da Bakon dundumin Dubarudu. Yadda kuwa wannan lamari ya wakana shi ne, ina neman kurkurido da za ta shigo da ni cikin kwaryar Haurubja daga garin Zube, sai kawai na […]

Bakon dundumin Dubarudu

A rana ta sili da manuniyar kasa ga watan Ukun-tutun-baba, na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, na hadu da Bakon dundumin Dubarudu. Yadda kuwa wannan lamari ya wakana shi ne, ina neman kurkurido da za ta shigo da ni cikin kwaryar Haurubja daga garin Zube, sai kawai na hango wani malami, na gaishe shi, sannan na bukaci ya nusar da ni inda zan samu shorido ko kurkurido da za ta karaso da ni gadar Baga. Da jin batuna, sai mutumin nan ya ce in dan tsahirta, ina nan tsaye kikam,sai ga shi tare da wata tsohuwa tukuf, ya ce ai sai mu rankaya tare.

Muna shiga cikin kurkurido, an dauki hanya, muna daf da zuwa garin Mabusa, sai kawai ya fara bijiro min da wani batu wai suna laluben inda za su fake, ta yadda da subahi sakaliyya, sai su tafi kasuwar Wasa-wasa, don neman dan uwansu da ke sayar da samfarerar dangatan Kasuwa. Da jin wannan batu,sai kawai na ji ban gamsu ba, musamman a irin wannan yanayi na ‘Ba tsaro, sai tsoro.’ Nan take na tursasa shi, har ya tabbatar mini da cewa, sun yi nufin zuwa garin Juwa-juwa da ke kan tafarkin zuwa garin Daidai. Kuma ya ce mini wai guzurinsa saura Hauro dari babban lauje. Jin haka kawai na fasko cewa, wannan Bakon Dundumin Dubarudu ne.domin bai kamata mutum ya yi balaguro har da tsohuwa tukuf ba, alhali bai san inda ya dosa ba.
Da ya kammala batutuwansa, sai kawai na umarci mai jan linzamin kurkurido da ya ja, ya tsaya, na biya ladar dakon su, sannan na kara masa Hauro dari babban lauje, na sa shi a hanyar zuwa garin Daidai, inda daga can zai lalubi hanyar zuwa Juwa-juwa, idan kuma an yi juwa-juwa da su, su suka jiwo.
Haurobiyawa hakika na dugunzuma cikin tashin hankali, ganin yadda wannan mutum ya yi ta walagigi da tsohuwa a hanyar babban birnin Haurobiya, wai a irin waskiyar batutuwansa,’ya yarda kurtun maganarsa na halo alalo. Sannan suna laluben matsugunnin dan uwansa mai cinikin samfarerar dangatan kasuwa.’
Batu na ingarman karafa, bai kamata a irin wannan zamani na wayewa ba, mutum ya sulmiyo daga Arewacin Haurobiya ba tare da isasshen guzuriba, kuma wajibi ne ya mallaki kurtun magana. Uwa-uba, lallai akwai bukatar mutum ya san inda ya dosa.don haka duk wanda ba shi da wani abin yi takamaimai a birnin Haurubja kada ya kuskura ya doso garin, domin akwai yiwuwar a karke da haure-haure da hauragiya.
’Yan makaranta, ina fatan kun fasko cewa, wannan bako da na hadu da shi a kan tafarkin zuwa birnin Haurubja ba Bakon Dubarudu ba ne, don bai bukaci matar dubarudu ta ba shi madubin dubarudu ya duba ba,ballantana ya gano inda ya kamata ya fuskanta; kai shi ma Bakon Dubarudun da aka sha ba mu labarinsa a lokacin da muke koyon watsattsake da buda wagagen littatafai a cikin yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare dasa-in-sa ba, an yi nuni da cewa, amsar da uwargidan Dubarudu ta ba shi, ita ce: Ko ni matar Dubarudu ban duba madubin Dubarudu ba, sai kai bakon Dubarudu ka ce in ba ka ka madubin dubarudu ka duba? Kuma shi ba Bakon-danlele ba ne,ballantana in ce ko ya taba jagorantar Majalisar Wakilan Rafkiya ta kasar Haurobiya. To, wane ne shi?
Wannan bako dai ga dukkan alamu, shi ne Bakon dundumin Dubarudu, kuma idan har bai yi sa’a ba, haka zai karke da dawurwuri, ya yi ta gararamba. Kuma idan aka yi rashin sa’a yaron can na bayan kango ya hango su, yana iya cewa, ku zo in sauke ku a cikin kangona. To ahir dinka GizBaba, irin wadannan baki, musamman a birnin Haurubja ga hukuma ake danka su.
Haurobiyawa, musamman Arewatawa, a daina barin gayaunar karkara, a sulmiyo cikin birane don neman gararuma. Domin idan gararuma ba ta samu ba, to za a karke da gararamba. Sannan duk wanda zai yi balaguro to ya nemi guzuri, in ma da hali ya nemi wanda zai ba shi gudunmuwar wuri, tunda a wannan zamani shi ne maganin dawurwuri. Kusan duk abin da mutum zai gudanar na kyautata walwalwar rayuwa, sai ka ji an ce, ‘lallai a yi ga wuri, ga waina.’
Don haka wanda duk bai sani ba, to ya yi tambaya, wanda kuwa ya sani,to ya nusar da masu bukatar sani. Ni dai wani malamina ya taba ba ni labarin wani mai tabin kwanya day a rikakai kawo a rumfar kasuwa yana cewa: “Ka riki ban sani ba,don mutane za su yi ta koya maika har sai ka sanil; idan kuwa ka riki na sani,to mutane za su yi ta tambayarka har sai ka dawo ba ka sani ba.’
Haurobiyawa babban abin da ke jefa al’ummar kasar nan cikin dawurwuri bai wuce yadda muke yin marhabin da kowane irin bakon tsari, ba tare da dora shi a kan mizanin awon alfanu da akasinsa ba. Shi yasa ake ta yi wa al’umma tsare-tsaren tsimin tsiya da ta’adin dukiya; ga zaman-takewa (kashin shakushe) da wasan Samson-siya-siya a dama-dama-da-kurda-kurdar siyasar damo-da-da-kura da diya. Lokaci ya yi da za mu rika yin marhabin da bakon da ya zo mana da dimbin alfanun rayuwa, sannan mu ingiza keyar duk wani mugun daji, don kada ya jefa mu cikin dawurwuri. Lallai mu kiyayi Bakon dundumin Dubarudu. Wanda duk yake son shiga wata alkarya, to ya je musu a matsayin bakon direban alli; ko bokan turai; ko mai sana’ar na-duke da daukacin wata sana’a da za ta bai wa mutum damar samun sa’a ko da birnin Sana’a’a.
Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya, ku sani ni ban zubar da hawayen Tenhiya ba. Domin lokacin da na kuduri aniyar yin balaguro, sai na sanya Mai sarautar Sara-da-daukar-dawainiya na birnin Tagadas ya sanar da mahukunta cewa za a yi bakon Dodo, kuma har zuwa lokacin da na isar garin Tenhiya muna ta yin batu a cikin kurtu. Kun ga ke nan ba zan iya amincewa da Bakon Dundumin Dubarudu ba, domin ba shi da tabaran hangen nesa da kusa. Ba kuma wani abu ya tabbatar da matsaya a cikinkaratun wasikar jakin dawa da na gida ba, illa sanin cewa, hukuma na iya damke shi, ta ce, ta kama mai tayar da kan adda a yamutsin Haramta Bobo da kwambon Bokoko; ko kuma ta ce ga mai safarar mutane.