Bakuncin Gizago a Jihar Zamfara
Rabona da shiga cikin birnin Gusau na Jihar Zamfara tun mulkin Yariman Bakura na farko, kodayake na sha zuwa, amma dai shigar shantun kadangare nake mata, domin kuwa nakan wuce in je Sakkwato, ba tare da na shiga kwaryar garin ba.A wannan karon, na niki gari a ranar Juma’ar da ta gabata, na tunkari birnin. […]
Rabona da shiga cikin birnin Gusau na Jihar Zamfara tun mulkin Yariman Bakura na farko, kodayake na sha zuwa, amma dai shigar shantun kadangare nake mata, domin kuwa nakan wuce in je Sakkwato, ba tare da na shiga kwaryar garin ba.
A wannan karon, na niki gari a ranar Juma’ar da ta gabata, na tunkari birnin. Babban makasudin zuwa Gusau kuwa shi ne, domin halartar taron ‘Dandalin Siyasa A Intanet’ karo na biyar, wanda Gwamnatin Jihar Zamfara ta dauki bakuncinsa.
A matsayina na wanda ya dade bai rakade birnin Gusau ba, sai na samu kaina a matsayin bako, wanda haka ya sanya al’amura da yawa suka zame mani abin al’ajabi. Na farko dai, na samu garin ya canza matuka daga yadda na san shi a baya. Na ga yadda aka shimfide shi da manyan tituna masu gida biyu da magudanun ruwa a kowane bangare. Haka kuma, na ga yadda sababbi kuma manyan gine-gine suka cika birnin, kamar kuma yadda na ga an dandashe mahada titunan da fitulun ba da hannu.
Game da hanyoyin nan kuwa, masu ababen hawa, musamman ma ’yan baburan Acaba, har ma da wasu masu motocin tasi, na ga yadda suke karya dokokin hanya kai tsaye. Na ga yadda suke yin tukin ganganci da wauta. Akwai lokacin da na zo shataletalen kusa da Gidan Gwamnati, fitilun bayar da hannu sun ba hanyarmu izinin tafiya amma sai ga shi ’yan Acaba da wasu kalilan din motoci sun shiga titi daga hannun da ke daura da namu (wanda kamata ya yi su tsaya). Bisa ga haka, saura kadan in kade wani mai babur amma Allah Ya kiyaye, na dauke kan motata da sauri. Da baicin taimako da agajin Allah, da yanzu labari ya cika gari, cewa Gizago ya kade dan Acaba, (Allah Ya kiyaye)!
Wani abu kuma da ya daukar mani hankali game da Jihar Zamfara shi ne, yadda na rika jin mutane suna yaba wa gwamnatinsu mai ci a yanzu, a karkashin Gwamna Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar, musamman suna cewa yana yi masu ayyukan raya kasa. Da nake magana game da titunan da na ga sun kayata birnin, shi ne wani ma’aikacin otel din da na sauka ya shaida mani cewa ai duk aikin gwamnan ne mai ci yanzu.
Al’amari na gaba da ya kara daukar mani hankali shi ne, abin da na tsinkaya a daren Lahadi, lokacin da aka gudanar da liyafar cin abincin dare tare da Gwamna Abdul’aziz Yari. An gudanar da liyafar ce a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara. Bayan an kammala cin abinci da abin sha, sai aka gayyaci gwamnan domin ya gabatar da jawabinsa. Jawabin nan nasa ne ya zama abu na gaba da ya doki zuciyata, ya daukar mani hankali matuka.
Gwamnan ya bayyana yadda yake tafiyar da al’amuransa, sannan ya yi bayani dalla-dalla game da hakkin da ke kansa, kamar kuma yadda ya tunatar da al’umma cewa su ma suna da hakki. Ya ta’allaka yadda ake samun matsaloli da yawa daga shugabanni a Najeriya da rashin sanin makamar aikin da ke kansu. Ya ce a wannan zamani da muke ciki, mafi yawan masu rike da madafun iko, suna samun kansu ne kawai a mulki, ba tare da sun shirya masa ba.
Game da haka, ya shawarci al’umma da cewa, duk wani abu da za su aikata, to su samu iliminsa tukunna. Mai mulki, ya yi kokarin sanin makamar aikin da ke gabansa.
Wani kalamin da gwamnan ya yi, wanda kuma ya dauki hankalina, shi ne inda ya ce dole ne mai mulki ya yi taka-tsan-tsan da mabiyansa, wadanda a mafi yawan lokaci sukan wuce makadi da rawa wajen zuga shugaba, su nuna masa cewa shi ne shugaban kowa kuma ya fi kowa. Gwamnan ya ce, a lokacin da shugaba ya biye masu, ya dauki wannan zuga da ingiza-mai-kantu-ruwa, to zai kasance mai girman kai. Idan ya yi haka, to barna za ta biyo baya.
Abu na gaba da ya daukar mani hankali a Jihar Zamfara, shi ne ganawarmu da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Zamfara, zakakurin mutum mai himma, Alhaji Ibrahim Muhammad (dan Madamin Birnin Magaji). A matsayinsa na daya daga cikin jami’an gwamnati da suka kasance masu masaukin baki a taron nan, bai nuna gazawa ba ko kadan. Duk inda ake wata hidima a taron nan sai ka gan shi tsamo-tsamo, ana tafiyar da al’amura da shi.
Saboda azamarsa, shi ya jagoranci membobin dandali da suka zo taron nan daga sassan kasar nan zuwa ziyarar gani da ido zuwa wasu muhimman ma’aikatu, domin shaida ingantattun ayyukan raya kasa da gwamnatinsu ta gudanar.
Kwamishinan da kansa ya jagorance mu zuwa Gidan Rediyon Jihar Zamfara, wanda ake kira da sunan Gidan Injiniya Mamman Maru. Mun ga sababbin na’urori na zamani, wadanda aka shaida mana cewa su ne ake yayi a duk fadin duniya. A takaice, ya shaida mana cewa, gwamnatin Abdul’aziz Yari ce ta kashe kudi har Naira biliyan daya, wajen kammala ginin gidan rediyon da kuma inganta shi da wadannan na’urori na zamani.
Ziyayar tamu ta dauke mu har zuwa Asibitin kwararru na Yariman Bakura, wanda shi ma aka inganta shi da na’urori na musamman, wadanda suka hada da na’urar gwajin yanayin sassan jiki, wadda da ita ake gwajin gano ciwon koda, ciwon suga da sauransu. Mun ga na’urar gwajin haihuwa ta zamani, mai aiki da hasken lantarki, wacce idan aka haska za a iya tantance yanayin ciki da sauran lalurorinsa. Mun ga na’urarori daban-daban, wadanda ya ce irinsu ne ake samu a manyan asibitocin zamani na kasashen duniya.
Kamar yadda ya ce, duk wani awo da ake gudanarwa a asibitin, Naira dari biyar suke amsa, domin saukaka wa talakawa. Ya ce gwamnatin tasu, ta kashe sama da Naira biliyan biyu wajen kammala ginin asibitin da kuma inganta shi da na’urori.
Daga nan ne kuma muka rankaya zuwa gadar boko, wadda kamar yadda Kwamishinan Watsa Labarai ya ce ake ginawa a halin yanzu. Wannan gada, hade da hanya mai nisan kilomita 75, za ta hada kananan hukumomin Talatar Mafara da Bakura da Maradun da Zurmi. Ya ce an bayar da kwangilar gina ta a kan Naira biliyan 7.1 kuma za a kammala ta cikin shekara uku, saboda muhimmancinta ga al’umma, musamman wajen bunkasa kasuwanci da noma da kiwo.
Mun yi wa Kwamishina dan Madamin Birnin Magaji Tambayar cewa, ta yaya ake samun dinbin kudin da ake aiwatar da wadannan muhimman ayyuka? Shi ne ya amsa da cewa: “Gwamnanmu ya dakile duk wasu hanyoyi na almubazzaranci da dukiyar al’umma, yana ririta dan abin da ake samu daga Gwamnatin Tarayya.”
Babu shakka na ji dadin bakunci na a Jihar Zamfara, musamman ma yadda na gana da Gizagawan Jihar Zamfara da na Jihar Sakkwato, su Yusuf Zamfara da su Kassim Lema da su M. A. Faruk da Nata’ala Babi da su Jamila Abubakar da Hussaina Abdullahi. Haka kuma, na hadu da zaratan Gizagawan Jihar Kaduna, irinsu Muntaka Abdul Hadi Dabo da Idris Barden Kubau da sauransu. Babu abin da zan ce, sai Allah Ya bar zumunci!