Bakuwar cuta ta hallaka yara sama da 40 a Jigawa

Maleriya ce – Gwamnati  Yaduwar wata cuta da ta rika hallaka kananan yara kuma aka ce ba a san ta ba tare da yayata bazuwarta a kafafen watsa labarai na ciki da wajen kasar nan yanzu an gano cewa cutar zazzabin cizon sauro ne wato maleriya.  Wakilimmu na Jihar Jigawa wanda ya ziyarci kauyen Dugus […]

Bakuwar cuta ta hallaka yara sama da 40 a Jigawa

Maleriya ce – Gwamnati 

Yaduwar wata cuta da ta rika hallaka kananan yara kuma aka ce ba a san ta ba tare da yayata bazuwarta a kafafen watsa labarai na ciki da wajen kasar nan yanzu an gano cewa cutar zazzabin cizon sauro ne wato maleriya. 

Wakilimmu na Jihar Jigawa wanda ya ziyarci kauyen Dugus da cutar ta fi yi wa illa, ya zanta da iyayen yaran da suka rasu da Dagacin Wangara da kauyen Dugus ke karkashinsa da kuma sauran hukumomi da lamarin kiwon lafiya ke hannunsu. 

Malam Usman Haladu wanda cutar ta kashe ’ya’yansa bakwai, ya ce ’ya’yansa bakwai da suka rasu sakamakon bullar cutar, sun hada da Hadiza da Salima da Rayya da Maryam da Abasiya da Habiba da kuma Umar 

Malam Usman Haladu wanda ya ce yana da mata hudu ya nuna takaici kan rashin asibiti a kauyensu inda ya ce suna yin tattaki ne zuwa wani kauye da ke Jihar Kano mai suna Larabar Zango, a kusa da karamar Hukumar Ajingi inda suke yin jinya da sayen maganguna domin bai wa ’ya’yansu kariya.

Ya kara da cewa wani lokacin kuma sukan je asibitin Jahun ko asibitin gaya da ke Jihar Kano domin a can ne ake amsarsu hannu bibbiyu saboda malaman asibiti suna yi marasa lafiya da danginsu wulakanci a asibitin Dutse.

Ya ce ko da larurar haihuwa ce sun fi amincewa su tafi babban asibitin da ke karamar Hukumar Jahun inda ake ba su kular da ta dace. 

Malam Usman ya ce ya kashe sama da Naira dubu 40 a kokarin ceto rayuwar ’ya’yansa bakwai, amma Allah bai sa suna da nisan kwana ba, saboda haka ya nemi gwamnatin Jihar Jigawa ta dube su da idon rahama wajen taimaka wa rayuwarsu da ta ’ya’yansu ta hanyar gina musu asibitin kwanciya ko da mai cin gado 20 ne.

Malam Usman ya ce galibin wadanda suka rasu kananan yara ne ’yan shekara daya zuwa shekara 2, kuma hakan ya tayar da hankalin jama’a saboda yaran ba sa iya yin magana, balle a iya sanin abin da yake damunsu sai dai likitoci ne kawai za su iya sani saboda aikinsu ne. 

Ya ce yanzu haka kananan yaran da suka rasu a garin sun kai 47, kuma akwai wadanda suke fama da cutar da suka kai yara 40 da suke kwance a gidajen iyayensu suna jinya. 

Sai dai ya yaba wa karamar Hukumar Dutse kan kai masu agajin gaggawa cikin hanzari bayan bullar cutar, ya ce ba don agajin da gwamnati ta ba su ba ba a san iyakacin yaran da za su rasu ba. “Ko a ranar Talatar da ta gabata sai da aka kai wadansu yara Babban Asibitin Dutse, kuma karamar hukumar ce ta kai su aka yi musu jinya, daya ma daga cikinsu tana asibiti an kwantar da ita saboda ta jiga ta sai da aka kara mata jini.

daya daga cikin matansa, mai suna HajaraZ ta ce wani abin mamaki shi ne duk wadda ta kamu ko ya kamu da cutar ba ya wuce kwana uku zuwa mako daya a duniya yake rasuwa, kuma kafin ya rasu sai ya daina cin komai kuma cikinsa yana kumbura kamar an kifa masa koko sai kuma ya barke da amai da gudawa daga nan sai yaro ya koma ga Allah. 

Shi kuwa Salisu Abdullahi wanda ’ya’yansa hudu suka rasu cewa ya yi bai taba ganin tashin hankali irin wannan lokaci ba, saboda a cikin kwana 14 cutar ta hallaka ’yar’yansa hudu da suka hada da Aliyu da Isah da Umar da kuma Shakuru Salisu kuma dukansu cikin lokaci daya suka kamu da cutar Allah Ya amshi rayukansu. 

Ya ce daga zazzabi cutar take farawa sai kuma cikin yaro ya kume ya daina cin abinci ya kasa yin komai sai kuma sai kirjinsa ya bankaro cikinsa ya yi kamar an kifa masa koko. Daga nan bayan kwana biyu zuwa uku sai yaron ya kama tari ya rika gudawa sai ajali ya zo masa. 

Malam Salisu ya ce ya sha dawainiya da ’ya’yansa wadanda dukansu ’ya’yan matansu biyu ne kuma ga shi yankin ba su da asibiti. “Muna fuskantar matsala saboda babu inda za mu je su samu lafiya sai mun shiga Jihar Kano saboda muna kan iyaka Jihar Kano ta fi kusa da mu,” inji shi.

Shi ma ya ce suna fuskantar matsala da malaman asibiti idan suka kai ’ya’yansu asibitin Dutse, don haka sun gwammace su shiga Jihar Kano ko su je asibitin Jahun inda mafi yawan likitocin ’yan Chaina ne suna duba su babu wata tsangwama. 

Ya ce a kokarin ceton rayuwar ’ya’yansa, ya kashe sama da Naira dubu 40, wajen sayen magunguna da na jigilar ababen hawa zuwa Ajingi da Larabar Zango da asibitin Jahun. Ya ce asibitin da yake kusa da su, asibitin Wangara, karami ne alhali irin wannan cutar dole sai an hada da manyan likitoci, saboda ta fi karfin kananan jami’an kiwon lafiya da suke zaune a asibitocin karkara. Sai ya nemi gwamnatin Jihar Jigawa ta dube su da idon rahama ta gina musu asibiti mai dan girma domin ceton rayuwarsu da ta matansu da ta ’ya’yansu domin fuskantar irin wannan cuta idan ta taso.

Da yake tofa albarkacin bakinsa Dagacin Wangara, Alhaji Aminu Abdullahi ya ce sun ga abubuwa masu tayar da hankali saboda bai samu labarin bullar cutar da wuri ba sai da abu ya kai wani hali, inda kimanin yara 20 suka rasu a garin na Dugus shi ne ya dauki waya ya sanar da hakiminsa shi kuma hakimi ya sanar da shugaban karamar hukuma sannan karamar Hukumar Dutse ta dauki matakin gaggawa a kan lamarin. 

Ya ce bayanan da suka samu kafin karamar hukumar da Hukumar Lafiya a Matakin Farko su kai wa jama’ar garin Dugus agaji yara sama da 45 sun rasu. “Sai dai dole a yaba wa gwamnatin Jihar Jigawa da karamar Hukumar Dutse da ita kanta Masarautar Dutse kan bayar da agaji don dakile yaduwar cutar,” inji Dagacin. 

Ya ce, bai samu labarin bullar cutar a kan lokaci ba ne saboda shi kansa mai unguwar Dugus ba ya da lafiya ga tsufa sai dai akwantar a tayar.

Dagacin ya ce binciken likitoci ya tabbatar da cewa cutar ba wata sabuwar cuta ba ce, malariya ce, mutanen garin ba su gano cutar ba ce da wuri har ta yi karfi a jikin yaran ta rika kashe su.

Ya ce wadanda suke dauke da cutar a garin na Dugus sun kai mutum 40 kamar yadda malaman kiwon lafiya suka labarta masa.

Ya roki gwamnatin jihar ta gina babban asibiti a garin Wangara, kuma ta gina wa kauyen Dugus asibitin haihuwa da bai wa kananan yara magani kyauta domin kare rayuwar mata da kananan yara. 

Ya yaba wa karamar Hukumar Dutse kan alkawarin da ta dauka na samar da asibiti a yankin domin kula da marasa lafiya a garin da kauyukan da suka kewaye da shi. Kuma ya ce shugaban karamar hukumar ya yi alkawarin za a samar da maganguna a asibitin domin raba wa mata masu ciki da kananan yara kyauta kamar yadda gwamnatin jihar ta yi alkawarin bai wa mata da yara magani kyauta a daukacin asibitocin jihar musamman manyan asibitoci, amma saboda abin da ya faru an saka asibitin yankin a cikin wadancan asibitoci domin taimaka wa mazauna yankin.

Da yake kare ma’aikatar lafiya a kan bullar cutar Daraktan Kula da kananan Asibitoci kuma Sakataren Hukumar Lafiya a Matakin Farko, Dokta Kabiru ya ce gwamnati tana sane da bullar cutar amma ba ya gari shi da Kwamishinan Lafiya da Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar da manyan jami’an ma’aikatar wadanda dukansu suke birnin Abeokuta don halartar wata bita a kan kiwon lafiya, saboda haka ya bukaci in tuntubi wani mai suna Dokta Bulangu a kan lamarin.

Lokacin da wakilimmu ya je ofishin Dokta Bulangu an shaida masa cewa ya tafi ofishin kungiyar Likitoci ta Jihar suna wata tattaunawa. Kuma daga baya da ya kira shi ta waya, sai ya shaida masa cewa ba ya da ikon yin magana da ’yan jarida sai dai ya nemi Kwamishina ko Dokta Kabir ko kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, sai ya kashe wayarsa. 

Shugaban karamar Hukumar Dutse wanda ya yi magana ta bakin Shugaban Sashin Kula da Tsabtar Muhalli da Ruwan sha na karamar hukumar, Malam Sa’idu Magaji Abubakar Dabi cewa ya yi shi ne ya jagoranci tawagar likitocin da suka kai wa jama’ar kauyen agajin maganin kuma sun rigaya sun shawo kan cutar. 

Ya ce cutar zazzabin maleriya ne ba wata cuta sabuwa ba, kuma sun shawo kan cutar an bai wa wadanda suka kamu da cutar magani an dakile yaduwarta.

Shugaban ya ce sun kai allurai da maganguna na ruwa da na kwayoyi da ruwan gishiri sun raba wa yaran da suka kamu da cutar, inda karamar hukumar ta kashe sama da Naira dubu 270, wajen sayen magangunan da ta kai agaji a garin na Dugus. Ya ce a kididdigarsu yara 40 ne suka rasu, kuma zazzabin ya yi musu illa ne saboda cutar ta raunana garkuwar jikinsu saboda rashin samun labarin bayyanar cutar a kan lokaci.

 Ya ce a kokarin da karamar hukumar ta yi an raba wa yara sama da 262 magungunan rigakafi domin magance tasirin cutar, kuma an shawo kan cutar, kuma duk da haka ranar Talatar da ta gabata an kwantar da yara shida a asibitin Dutse aka yi musu karin ruwa aka ba su maganguna. “daya daga cikinsu mai suna Zainab Jafaru har yanzu tana asibitin Dutse saboda an yi mata karin jini.

Daga nan ya shawarci mutanen garin Dugus da kewaye su rika kula da tsabtar muhalli tare da tura ’ya’yansu zuwa makaranta domin su koyi kiwon lafiya. Kuma ya gargadi mutanen kauyen da su rika zuwa asibiti a kan lokaci kuma su shaida wa hukuma idan suka ga wata sabuwar matsala da ba su saba gani ba a kan lokaci.