Bakuwar cuta ta kashe mutane 13 a Zamfara

Akalla mutane 500 sun kamu da bakuwar cutar a Zamfara da Sakkwato

Bakuwar cuta ta kashe mutane 13 a Zamfara

Adadin mutanen da suka rasu sakamakon kamuwa da wata bakuwar cuta ya karu zuwa 13 a Jihar Zamfara.

Akalla mutane 505, akasarinsu mata da kananan tara ne aka kai asibiti sakamakon kamuwa da cutar a kananan hukumomin Gusau, Maradun da kuma Shinkafi a jihar.

Haka zalika an samu bullar cutar a Jihar Sakkawato a kananan hukumomin Isa da Zurmi.

A watan Fabrairu aka fara samun bullar bakuwar cutar a kauyen Tsibiri da ke Karamar Hukumar Maradun.

Wani mazaunin Tsibiri ya ce daga lokacin “Zuwa ranar Lahadi 12 ga May, 2024, mutane 228 ne suka kamu da cutar a kauyen.

“An kai wasu daga cikinsu Babbar Cibiyar Hana da yaduwar Cututtuka ta Shehu Shagari da ke Gusau, sabobda tsanin da abin nasu ya yi.

“Wadanda nasu ke da sauki kuma an ba su magani an sallame su a Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHC) da ke Tsibiri.

“An Shinkafi, a watan Afrilu aka fara samun bullar cutar kuma kawo yanzu ta kashe shida daga cikin mutane 100 da ta kai su PHC.

Sama da 60 daga cikin mutanen da suka kamu a Shinkafi suna cikin mawuyacin hali, kuma an tura su zuwa Cibiyar Shehu Shagari,” in ji shi

A cewarsa da alama cutar tana yaduwa zuwa makwabtansu don haka akwai bukatar gwamnatocin jihohin biyu su dauki matakan dalike ta.

Kwamishinar lafiya ta Jihar Zamfara, Dokta Aisha Anka, ta ce alamomin bakuwar cutar sun hada da ciwon mara, zubar da yawu, kumburin hanta, zazzabi da jin kasala.

A cewarta, cutar na da alaka da shan gurbataccen ruwa kuma Cibiyar Shehu Shagari na aiki haikan domin gano musabbabin cutar da dabarun magance ta.

Kwamishinar ta kara da cewa tuni aka aika samfurin kwayar cutar zuwa dakunan gwaje-gwaje da ke Abuja da Legas domin gudanar da bincike.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos