Bakuwar cuta ta yi ajalin mutum 5 a Tanzania
Shugabar Tanzaniya ta alakanta bullar wadannan cututtuka da “habaka mu’amala” tsakanin mutane da namun daji.
Hukumomi a Tanzania sun ce wata bakuwar cuta ta kashe mutum akalla biyar a Arewa maso Yammacin kasar.
Rahotanni kuma suna cewa wasu mutum bakwai sun kamu da cutar a lardin Kagera, inda hukumomi suka tura tawagar likitoci domin binciko da kuma gano cutar.
- Yadda jadawalin kwata final na Champions League ya kasance
- An yi garkuwa da dan takarar mataimakin gwamna
Jami’an lafiya a kasar sun ce basu taba gani irin cutar ba.
Alamomin cutar sun hada da tari da ciwon kai da kasala da kuma zubar jini, a cewar Babban Likitar Gwamnati, Tumaini Nagu.
“Gwamnati ta hada tawagar kwararrun likitoci da tura su zuwa yankin domin gudanar da bincike da nufin gano ta,” in ji Farfesa Nagu.
Ta bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su kuma guji mu’amala da wadanda suka kamu da cutar.
A watan Yulin bara, an samu mutum 20 da suka kamu da wata bakuwar cuta a lardin Lindi da ke Kudancin kasar, inda uku suka mutu.
Shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan ta alakanta bullar wadannan cututtuka da “habaka mu’amala” tsakanin mutane da namun daji sakamakon gurbacewar muhalli.