Bakuwar dabba ta kashe raguna 6 a Abaji

Jama’ar Unguwar Sokodabo a karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja sun fada cikin fargaba bayan wata bakuwar dabba ta kashe raguna 6 a unguwar. Wani mazaunin unguwar Aliyu Usman ya bayyana cewa, ragunan an killace su ne a wajen da ake kiwon su, bayan wayewar gari sai mai ragunan ya tashi samu […]

Bakuwar dabba ta kashe raguna 6 a Abaji

Jama’ar Unguwar Sokodabo a karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja sun fada cikin fargaba bayan wata bakuwar dabba ta kashe raguna 6 a unguwar.

Wani mazaunin unguwar Aliyu Usman ya bayyana cewa, ragunan an killace su ne a wajen da ake kiwon su, bayan wayewar gari sai mai ragunan ya tashi samu ragunan duk a mace.

Aliyu Usman ya ce, dabbar da ake zargi da kashe ragunan ta jiwa ragunan rauni ta hanyar shan jinin su. Wakilinmu da ya ziyarci unguwar ya samuragunan a mace kuma hanjin ragunan a waje.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta