‘Bala mai ji da kai’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe, yaya hutu? Tare da fatan ana nazari a gida. A yau na kawo muku labarin ‘Bala mai ji da kai’. Labarin ya yi nuni ne ga mahimmancin rike sirri a rayuwa. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi. Bala wani talaka ne talaka wanda yake ji da kansa. Har ’yan […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe, yaya hutu? Tare da fatan ana nazari a gida. A yau na kawo muku labarin ‘Bala mai ji da kai’. Labarin ya yi nuni ne ga mahimmancin rike sirri a rayuwa. A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi.
Bala wani talaka ne talaka wanda yake ji da kansa. Har ’yan kauyen sun gane cewa ba kowa ne yake amsa masa sallama ba sai masu kudi ko kuma kyawawan mutane.
Bala na da mata daya wacce a kullum take masa kashedin canza halinsa don ya koma na kirki.
Ran nan bayan ya karya kumallo sai ya yi sallama da iyalinsa cewa zai fita nemo abin cefane. Ya yi ta yawo a cikin daji har ya rasa hanyarsa zuwa gida. Ya yi ta zagaya daji har ya gaji bai gane hanyar fita ba sai ya yanke shawarar ya dan kwanta ya huta. A hakan bacci ya kwashe shi har dare ya yi bai farka ba.
Can sai ga wadansu wadanni kimanin 15 wadanda suka ciccibe shi shi zuwa cikin wani kogo. Yana farkawa sai ya ga wadannan wadanni a kansa sai ya tsorata. Wadanni suka kwantar masa da hankali tare da ba shi abinci wanda bai taba cin irinsa a rayuwarsa ba. Sannan suka hado shi da zinarida lu’u lu’u sannan suka yi masa kashedin kada ya kuskura ya fadawa kowa inda ya samo wannan dukiyar. suka nuna masa hanya ya koma gida.
Yana isa gida sai girman kai ya karu. Matarsa ta yi da shi ya fada mata inda ya samo dukiyar yaki. Da ta fara yi masa zargin sata sai ya kwashe labari ya fada mata. Bai rufe baki ba sai zinaren da lu’u lu’u suka bace ya koma tsabagen talaka. Hakan ta sa ya yi ta cizon yatsa tare da yin nadama.